Saturday, 26 January 2019

DAGA MAJALISAR ANNABI













HIRA DAGA
         
Majalisar Annabi Muhammad  (SAW)
.
     Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta

Yace: "Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?

Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_
1: zama a gaban ka,
2: kallon ka,
3: ciyar da dukiya ta gare ka.

Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki
Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?

Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_
1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne,
2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,
3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci.

_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_

_Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_
1: ciyar da abinci ga mabukaci,
2: yada sallama,
3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_

_Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_
1: Azumi a lokacin rani,
2: Karrama bako,
3: yakar abokan gaba da takobbi.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_

_Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_
1: yunwa,
2: jinya,
3: mutuwa.

_Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_
Sai Aba zarri yace:

*ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,
*ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi,
*ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na

_A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_
1: isar da sako,
2: bayar da amana,
3: son nakasassu.

_Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah da sahabbai tayi dadi, harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku_
1: harshe mai ambatonSa,
2: zuciya mai tsoronSa,
3: jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri.

_Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah Girma da tsarki sun tabbata Allah_ Adu'o'i guda uku kada ku manta su acikin sujjadarku..
"Ya Allah ina rokonka kyawawan halaye".
"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace"
"Ya ALLAH mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka"

Lalle wannan ya cancanta ku tura zuwa ga waninku domin ya amfana.

Dauki darasin ka a cikin wannan hadith, ka aikata shi, za ka yi nasara.

Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne, yi kokari ka fita a sahun farko na daliban makarantar.

Kayi sharing a sauran groups domin yan uwa sugani su amfana

Wednesday, 11 November 2015

GATA NAN GATA NAN KU





 GA TA NAN, GA TA NANKU:
TAZO MUJITA:

Akwai wani mutum da ke zaune a wani gari mai suna Raqumawa tare da matarsa da 'ya'yansu su goma sha daya.
Rannan sai matarsa ta haifi da namiji, ya zama na goma sha biyu.
Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana, ya ce wa uwarsa: "Kada ma a yi wahalar rada mini suna, domin sunana dan-kutun-gayya." Ya qara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinqa hawa.


Iyayen suka yi haka, jama'ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi. Ana nan, ana nan, sai wata rana yayyen dan-kutun-gayya suka shirya za su gidan wata mata da suka saba zuwa gidanta hira da 'ya'yanta su goma sha biyu.



Sai dan-kutun-gayya ya ce zai bi su amma babban wansu ya hana shi bin su. Amma ya bari sai da yayyen suka tafi, sai ya bi su a baya. Da isar su gidan, sai matar ta yi musu maraba; ta yi musu shimfida, suka zauna; ta kawo musu abinci mai dadi suka ci, suka fara hira. Amma fa duk zuwan da suke yi gidan, ba su san cewa matar nan Dodanniya ce ba.
Suka zauna suna ta hira kamar yadda suka saba kullum. Kuma duk sadda suka yi barci a gidan, Dodanniyar kan tashe su, su tafi gida.


 Ashe duk wannan dabara ce take yi don su saki jiki da ita, wata rana ta cinye su. Kuma tuni ta yi tanadin manyan tukwanen dafa su, ta sha romo. To, a daren da suka je tare da dan-kutun-gayya ma, duk sauran sun yi barci in ban da shi.



Can cikin dare sai ya ji ana wasa wuqa, sai ya ce a ransa: "A'a, lafiya kuwa?" Sai ya kwanta ya yi kamar yana barci. Da aka dan jima sai ya ga Dodanniya tana sanda, har ta shiga wajen yara. Da ya ga lallai ta nufi yayyensa, sai ya yi tari da qarfi. Da ta ji tarinsa, sai ta koma da sauri.



Da aka jima, sai ta sake dawowa; shi kuwa dan-kutun-gayya ya qara yin tari, ta koma.
A zuwanta na uku ne fa da ta ji tarin dan-kutun-gayya, sai ta boye wuqar ta leqo ta ce: "Kai dan samari ba ka barci ne?" Sai ya ce: "Ai ni ba na barci in ba a kan rairayin qorama mai sanyi ba." Da ta ji haka, sai ta dauki masaki ta tafi neman rairayin qorama. Kafin ta dawo sai dan-kutun-gayya ya fito da wata 'yar batta, ya bude bakinta, ya zazzago wani magani, ya matsa kusa da wutar da ta hura, ya barbada maganin nan a cikin wutar, sai wani hayaqi ya tashi. Da 'ya'yan Dodanniya da yayyensa suka shaqi wannan hayaqi, sai barcin da suke yi ya qara nauyi.



Nan da nan dan-kutun-gayya a cikin sauri irin na hatsabiban mutane ya bi ya tube wa 'ya'yan Dodanniya kayan jikinsu, ya sanya wa yayyensa. Kuma ya tube wa yayyensa nasu kayan, ya sanya wa 'ya'yan Dodanniyar. Da ya gama wannan aiki sarai, sai ya kwanta, ya shiga jira.
Can sai Dodanniya ta dawo, ta kawo rairayi ta ba dan-kutun-gayya. Sai ya ce: "Yawwa Iya, na gode. Yanzu zan yi barci." Da aka jima sai Dodanniya ta dawo da wata sharbebiyar wuqarta a hannu, ta iske dan-kutun-gayya ya yi barci. Nan da nan cikin gaggawa da qeta ta bi duk 'ya'yanta ta yanke, tana zaton samarin da sukan je hira gidanta ne.



Amma ba ta yanka dan-kutun-gayya ba saboda ta ga shi qarami ne. Ta qyale shi, da nufin kiwata shi ya yi qiba. Da Dodanniya ta fita za ta fara shirin kwashe naman da take zato ta samu, sai dan-kutun-gayya ya zaro battar nan tasa ya sake barbada garin maganin nasa a kan wuta.



Kafin qifta ido, hayaqi ya murtuke daki. Cikin gaggawa ya tashi yayyensa, ya gaya musu abin da ya faru, kuma ya ce su yi maza-maza su gudu gida. Ya ce shi zai bi su da gari ya waye, kada su jira shi. Take suka sulale, suka gudu. Da gari ya waye, sai Dodanniya ta zo za ta fara tattara wadanda ta yanka, a zatonta 'yan uwan dan-kutun-gayya ne. Yana ganin ta sai ya kada battarsa, sai ga ragonsa ya zo ya harari Dodanniya, yana yi mata kallon raini ya ce: "To, wadannan fa 'ya'yanki ne kika yanka, ba 'yan uwana ba." Da ta lura da haka, sai ranta ya baci ta yi wani qaraji, ta yi wuf ta kai masa bara za ta cafke shi, sai ya baude. Ta sake rarumo shi, amma sai ya dare bayan ragonsa. Rago kuwa kamar ya san zancen, sai ya kama sukuwa kamar walqiya, ya tsere mata fintinkau, ya bar ta sororo a cikin baqin ciki. Dodanniya ta dauko dan magurjinta na tsafi, ta bi 'ya'yanta tana buga wa kowannensu a ka.



Nan da nan namansu ya zama na tumakai, ta soye suka cinye ita da autarta. Daga nan ta yi alqawari sai ta rama qetar da dan-kutun-gayya ya yi mata
Bayan 'yan kwanaki, sai Dodanniya ta je bakin garin su dan-kutun-gayya ta rikide ta zama kanya kuma ta kwatsa 'ya'ya da yawa, har sun kusa nuna. Da yaran gari suka ga kanyar sai suka yi murna. Da ta nuna, sai wasu daga cikinsu suka dinga kado 'ya'yan suna sha.



Har dai wata rana yara da yawa suka hau kanta suna diba. Da Dodanniya ta ga haka sai ta tashi sama da su, ba ta tsaya ba sai a gidanta. Nan da nan ta gaya wa autarta cewa nama ya samu. Sai ta umurce ta da ta wanke tukwane. Tana kuwa cikin wanke tukwane sai dan-kutun-gayya ya ji labarin abin da ya faru, sai ya rikida, ya zama dan maraqi, ya je gidan Dodanniya. Da zuwansa sai ya fara cin shuke-shuken da ke gidan, watau dai yana yi mata barna.



Yana cikin wannan barna sai Dodanniya ta ce wa yaran da ta sato, su je su kori dan maraqin mai yi mata barna. Da ya ga sun doshe shi sai ya qi gudu, amma da suka zo dab da shi, sai ya dan gudu ya dan matsa gaba kadan kuma ya ci gaba da barna. Yara kuma suka dan matsa kusa da shi, ya dan qara gaba kadan.



Haka dai ya dinga jan su, har sai da suka yi wa Dodanniya nisa. Sai ya rikida ya zama mutum, ya ce da yaran nan su hanzarta su gudu. Ya jaddada musu cewa idan ba su gudu ba, Dodanniya za ta cinye su. Da suka ji haka, sai suka sheqa da gudu, suka koma garinsu, suka gaya wa iyayensu abin da ya faru.



Shi kuwa dan-kutun-gayya sai ya hau ragonsa, ya koma gidan Dodanniya. Da ya tabbatar ta gan shi, sai ya yi mata gwalo ya ce mata: "Na kubutar da yara daga sharrinki, sun koma wurin iyayensu. Ni ne dan-kutun-gayya na yi miki gayyar tawa, wadda ba za ki iya ramawa ba har abada."



Wannan abu da dan-kutun-gayya ya yi wa Dodanniya da maganar da ya gaya mata, suka sa ta shiga tunani da qulla yadda za ta dauki fansa a kansa.
Ana nan sai Dodanniya ta rikida, ta zama mace kyakkyawar gaske, ta dauki wani adudu ta je cin kasuwa. Masoya suka yi ca a kanta, kowa yana so ya aure ta amma ta ce ba wanda za ta aura sai wanda ya bude wannan adudun. Samari da yawa suka gwada amma duk suka kasa. Bayan 'yan kwanaki, har samari sun fid da rai, sai daya daga cikin yayyen dan-kutun-gayya ya ji labari, ya bincika inda take a kasuwa ya je kuma ya gan ta, sai ya ji yana son ta. Ita kuma Dodanniya ta gane shi, saboda haka sai ta yi tsafi ta yadda idan ya gwada bude adudun zai bude.



Da zuwansa kuma ya gwada sai adudun ya bude, mutane suka yi ta mamaki, shi kuma ya yi murnar samun kyakkyawar mata.


Aka daura aure, ba ta jima ba ta tare a gidansa. Amma bayan 'yan kwanaki sai ta qwaqwale wa mijin ido daya, ta tafi da shi ta bar shi da jinya. Dan-kutun-gayya da jin wannan aika- aikar, ya tabbatar da cewa Dodanniya ce. Don haka ya quduri aniyar sai ya dauko fansar abin da ta yi wa yayansa.



Sai ya rikida ya zama Bafilatana, ya dauki nono, ya je gidanta talla. Da isar sa sai autar Dodanniya ta fito ta saya. Shi kuma ya yi mata araha. Kullum sai ya kai tallar nono, Dodanniya ba ta gane gogan ne ba.



Da haka har Dodanniya ta saba da Bafilatana qwarai da gaske. Wata rana sai Bafilatana, watau dan-kumale ya zo gidan Dodanniya a fusace. Dodanniya ta tambayi Bafilatana dalilin fushinta, sai ta ce: "Wani mutum wai shi dan-kutun-gayya yake zuwa yana kashe mana shanu. Ga shi yanzu duk sun kusa qarewa." Dodanniya ta ce: "Ke ba sunansa dan-kumale ba, sunansa dan-kutun-gayya.



Mugun mutum ne. Ba shanunku kadai ba, ku kanku ma ku yi hankali da shi. Ni 'ya'yana goma sha daya ya sa na kashe.



Kwanan nan ma na kusa makantar da dan uwansa. Kin ga idon yayansa da na qwaqule." Sai Bafilatana ta ce: "Tir da ganin idon lalatacce." Sai Dodanniya ta ce: "Yau saura kwana uku ma in ba kyanwata idon mugun ta cinye." Bafilatana ta ce: "Kash, da idon nan zai yi wa qanena daidai da kin ba ni shi. Shekaranjiya saniya ta harbi idonsa daya ya fashe ya tsiyaye." Cikin doki da qeta Dodanniya ta ce: "Af, don wannan ai sai in ba ki." Da jin haka sai Bafilatana ta yi farat ta ce: "Ai ko na gode." Dodanniya ta qara yiwa Bafilatana gwaninta, sai ta gaya mata yadda za ta sa masa idon, ta ce: "A nemo qwayayen kifi guda bakwai da hantar baqin kare da kiyashi guda bakwai da kaucin marke; a shanya su bushe, sai a niqa, a rinqa sa masa a gurbin idon har kwana uku.



A rana ta hudu sai a sa idon, zai zauna daram." Bafilatana, watau dan-kutun-gayya ta amshi ido, ta yi godiya. Da ta gusa kadan sai ta tube kayan Fulani, sai ga dan-kutun-gayya ya bayyana. Sai ya yi wa Dodanniya gwalo ya ce: "Kin ga ni ne dan-kutun-gayya." Sai ya yi wani hatsabibanci ya bata, Dodanniya ta daina ganinsa. Bai tsaya a ko'ina ba sai gida.
Da ya isa ya yi yadda Dodanniya ta kwatanta masa, idon yayansa kuma ya zauna daram, kamar ba a taba qwaqule shi ba.



Rannan kuma sai Dodanniya ta rikida ta zama kyanwa. Ta kama hanya ba ta tsaya ko'ina ba sai gidan su dan-kutun-gayya.


Da shigarta sai ta iske shi yana barci, sai ta lababa, har ta kai kusa da shimfidarsa. Sai ta yi wani karatu irin na tsafinta, ta tofa masa a fuska, sai ya zama bera, sai ta dauke shi ta kai gidanta, ta sa shi a quryar daki.



Daga nan ta yi masa wani tofin, ya koma mutum. Ita kuma ta rikida ta zama mutum, sai ta harare shi, fuskarta murtuk, tana cike da fushi, ta ce: "dank-utun-gayya, yau fa ga ni ga ka, qaryarka ta qare." Dan-kutun-gayya bai tsorata ba kuma bai ce mata komai ba. Can da Dodanniya ta dan huta sai ta sa autarta tsaron dan-kutun-gayya; ita kuma ta kama hanyar kasuwa sayen kayan yaji wanda za ta dafa shi da shi.
Tafiyarta ke da wuya sai dan-kutun-gayya ya yi wa 'yar auta dabara, ya karbe kayan jikinta ya sa, ita kuma ya sanya mata nasa.


Can sai ya ji motsin Dodanniya ta dawo, ya zabura, ya tarye ta yana kwaikwayon maganar 'yar auta, yana yi mata maraba.


Bayan wani dan lokaci kuma sai ga 'yar a cikin kayan dan-kutun-gayya tana yi mata maraba. Sai dan-kutun-gayya ya dubi Dodanniya ya ce mata: "Ga munafukin nan dan-kutun-gayya yana nunawa wai shi ne ni 'yar autarki har da cewa, Sannu da zuwa inna.' Yau dai qaryarsa ta qare." Sai Dodanniya ta ce: "Lallai kam, bar ni da lalatacce!" Nan take ta yi wuf ta shaqo 'yarta, ta sa wuqa ta yanka. Tana gama yanka autarta sai dan-kutun-gayya ya buga tsalle gefe, ya kwance zannuwan da ya daura, ya dubi Dodanniyar nan ya ce: "'Yar auta kika yanka, ni ko ni ne dan-kutun-gayya gwanin gayya.



Na yi miki gayyar tawa!" Yana gama fada mata haka sai ya yi wal, ya bace.
Dodanniya ta kama 'yarta ta tube kayan jikinta, sai ta ga lallai kuwa autarta ce ta yanka. Nan take sai ta hadiyi zuciya ta mutu.


Qurunqus! Qarshen wannan tatsuniya ke nan, kuma tana dauke da darussa kamar haka:

1. Qaunar juna da son 'yan uwa kan qara wa juna danqon zumunci, kuma ya kubutar da su daga duk wani sharrin maqetaci, kamar dai yadda dan-kutun-gayya da 'yan uwansa suka tsira daga Dodanniya.
2. Haka kuma, tatsuniyar nan ta fassara mana Karin maganar nan da ke cewa, mugunta fitsarin faqo ce, wanda ya yi ta take koma mawa kansa.
Zaka iya tunani wani abu wada tatsuniyar nan ta koya mana?????

KYAKYAWAN KARSHE KASHI NA DAYA







Dukkan yabo da godiya da kirari da jinjina sun tabbata ga Allah Ta'ala, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa.


Tsira da amincin Allah su tabbata ga ManzonSa, Alayensa da Sahabbansa da mutanen gidansa da wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.


Bayan haka, 'Yan uwa ko shakka babu, yana daga cikin Rahamar Allah Ta'ala Ya kasance bawa ya dace da kyakkyawar karshe a rayuwarsa.


Da haka ne ya sanya na ga dacewar in janyo hankalin kaina da sauran' yan uwana Musulmi domin fatan dacewa da wannan tagomashi.



MENE NE KYAKKYAWAN KARSHE?: 

Kyakkyawan karshe, shi ne ya kasance Allah Ta'ala Ya datar da Bawa kafin mutuwar shi ya zamto ya nisanci dukkan wani abu da yake fusata Allah, da tuba daga zunubai da sabo, sannan ya zamto Bawa ya fuskanci ayyukan da'a da ayyuka na alheri, sannan ya zamto Allah Ta'ala Ya karbi rayuwar Mutum a haka.


Daga cikin abin da yake nuni akan abin da muka ambata, shi ne hadisin da ya inganta daga Anas Bn Malik, Allah Ta'ala Ya kara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, ya ce: "Idan Allah Ta'ala Ya na nufin bawanSa da alheri, sai ya yi aiki da shi" sai suka ce: ta yaya (Allah) Zai yi aiki da shi?, sai ya ce: "Zai datar da shi da ayyuka nagari kafin mutuwarsa".


Imamu Ahmad ne ya ruwaito 11625 da Imamut Tirmizy 2142 sannan Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy ya inganta a cikin Silsilatus Sahihah 1334.


Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Idan Allah Mai Girma da Daukaka Yana nufin Bawa da alheri, sai ya dogar da shi" sai aka ce ya zai dogar da shi?, sai ya ce: "Allah Mai Girma da Daukaka zai bude masa aiki na alheri wanda zai rinka yi kafin mutuwarsa, sannan a dauki ransa yana wannan aiki". Imamu Ahmad ya ruwaito 17330 kuma Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy ya inganta a cikin Silsilatus Sahihah 1114.
Kyakkyawan karshe yana da alamomi...


Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala.

GIRMAN KAI KASHI NA SHA TARA

GIRMAN KAI KASHI NA SHA TARA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 8:

Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?

Ci gaba...

3 - Mai girman kai don ya na da ilimi: Duk wanda yake girman kai don ilimin da Allah ya bashi, kuma yake son Allah ya raba shi da wannan girman kan, sai ya kalli abubuwa kamar haka:

Abu na farko sai ya kalli cewa abin da bai sani ba ya fi abin da ya sani yawa, kuma akwai daruruwan mutane da su ka fishi ilimi nesa ba kusa ba. Kuma ya kalli misalin Annabi Musa (as), a lokacin da aka tambaye shi wane ne mafi ilimi a ban qasa? Sai ya ce: “ni ne." kuma Ya fadi haka ne saboda ya na da yaqini cewashi Annabi ne Mursali, a lokacinsa babu wanda ya ke da sani kamrsa. Amma duk da haka sai da Allah Madaukakin Sarki ya jarrabe shi, ya umarce shi da ya je mahadar koguna biyu inda a nan ne ya hadu da Khadir. Haqiqa yadda qissarsu ta kasance, akwai izina ga duk mai hankali da Allah ya ba shi ilimi akan kada ya dogara da abinda ya sani sai dai ya maida Ilimi zuwa ga Allah.

Abu na biyu shi ne; mai ilimi ya kalli tsawatarwar da Allah Madaukakin Sarki ya yi akan girman kai, kuma ya dubi narkon da Allah ya tanada don ma su wannan hali da jan kunnen da ya yi akai. Kuma mai girman kai da taqama don ilimi ya kalli qarshensa, domin akwai ranar mutuwa, imma ya yi kyakkyawan qarshe ya sami babban rabo, ko kuma ya yi mummunan qarshe, ya tabe, ya yi asara. Haqiqa kyakkyawan qarshe yana tabbata ne ga masu kiyaye dokokin Allah. Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Haqiqa kyakkyawan qarshe ya tabbata ga ma su taqawa." - (Suratul Kasas, aya ta 83).

Kuma mai ilimi ko wane iri ne ya kalli cewa shi fa abin misali ne a gurin wasu, abin da yake aikatawa shi wasu za su kwaiqwaya, kuma Manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda ya sunnanta wa mutane wata mummunar hanya; laifinsa yana kansa da kuma laifin wanda ya yi aiki da ita bayan sa, ba tare da an tauye mu su komai a cikin laifinsu ba." - (Muslim) 1017).

Don haka, lallai wadanda Allah ya ba su ilimi, su ji tsoron Allah, su kiyayi wannan mummunar dabia don kada iliminsu ya zamanto musu asara duniya da lahira. Allah ya kiyaye mu baki daya.

4- Mai yin girman kai don mulki ko wata sarauta da Allah ya ba shi:

In har yana son magance wannan, sai ya kalli wadanda yake mulkarsu, akwai wadanda sun fi shi ilimi, wadansu sun fi shi hikima, wadansu sun fi shi qarfi, wadansu sun fi shi kyawun halitta, wadansu sun fi shi dukiya, uwa uba wadansu sun fi shi tsoron Allah da riqo da addini.

Ashe Ubangiji Madaukakin Sarki da ya ba shi wannan mulkin ba don ya fi kowa ba ne, sai dai kawai don ya jarrabe shi, a cikin rayuwarsa ya ga yadda zai yi.

Har ila yau, ya yi izina da lura, akwai wadanda sun fi shi jin mulki da jin sarauta, sun fi shi iko, amma yanzu su na cikin kabari sai abin da suka aikata, da shi za a saka musu. Ya tuna ranar da za a sa shi a cikin likkafani a binne shi a qarqashin qasa, ya ruve ya zama abincin tsutsa.

Idan ya yi izina da wadannan abubuwa da su ka gabata sai ya tuba zuwa ga Allah (swt), ya yi nadamar abin da ya aikata a baya tun kafin ajali ya zo ma sa. Ko Allah ya jarrabe shi kafin mutuwa a kwace mulkin a wulaqanta shi a kulle shi a kurkuku da abinda ya yi kama da haka, Allah Maxaukakin Sarki ya ce: Ka ce: "Ya Allah mamallakin mulki, kana bayar da mulki ga wanda ka ga dama, kuma kana qwace mulki daga wanda ka ga dama, kuma kana daukaka wanda ka ga dama, kuma kana qasqantar da wanda ka ga dama. Dukkanin alheri a hannunka yake. Haqiqa kai ne mai iko akan dukkan komai."

Allah ya kare mu daga sharrin girman kai.

5- Mai yin girman kai don Allah ya ba shi qarfi na gangar jiki: Lallai wannan ya sani cewa: duk qarfin sa ba zai buwayi Allah ba, kuma ba zai tsinana ma sa komai ba, kamar yadda qarfi bai tsinanawa Adawa da Samudawa komai ba.

Mai wannan hali ya sani cewa Allah ne ya ba shi wannan qarfin, kuma idan ya so zai karbe shi lokaci daya kamar yadda ake ganin misali a gurin marasa lafiya da tsofaffi. Kuma mutum zai gane cewa qarfinsa ba komai ba ne idan ya kalli manyan dabbobi wadanda sun fi shi qarfi, amma Allah ya dora mutum akansu. Kuma ya kalli qananan qwari wadanda kan addabe shi duk da qarfin na sa. Kamar sauro ko cinnaka su cije shi, ko quda ya shigar ma sa maqogwaro, ko kiyashi ya shigar ma sa kunne. Ba tare da qarfin na sa ya amfana ma sa komai wajen hana su ba.

Yin wannan tunanin zai taimakawa mai girman kai ya daina in Allah ya yarda. Allah ya fahimtar da mu baki daya.

Sai mun hadu a fitowa ta 20 da yardar Allah.

GIRMAN KAI KASHI NA SHA TAKWAS

GIRMAN KAI KASHI NA SHA TAKWAS

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 8:

Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?

Ci gaba...

C. Hanyoyin magance girman kai da ji-ji-da-kai da taqama:

1- Mai yin girman kai domin asalinsa. Wannan zai tsaya ne ya kalli nasabarsa ta haqiqa, wato asalin sa digon maniyyi ne. Duk kuwa wanda asalin sa maniyyi ne to girman kai bai dace da shi ba, domin asalin nasa ba komai ba ne face qazanta. Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Shin ba mu halicce ku daga ruwa wulaqantacce ba? Sai mu ka sanya shi a cikin mahaifa abar kawwamewa?” - (Suratul Mursalat, aya ta 20 -21).

A wata ayar kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Dan Adam ya kalli da mene ne aka halicce shi? An halicce shi ne daga wani ruwa mai tunkudowa (shi ne digon maniyyi wanda yake fitowa a lokacin saduwa)." - Suratul Dariq aya ta 5 - 6.

Wadannan ayoyi da makamantansu su na nuna mana cewa, idan yana taqama da asali ne, to asalinsa maniyyi ne wulaqantacce.kuma kowane dan Adam daga wannan asalin yake, babu mai girma sai wanda Allah ya girmama.

2- Wanda ya ke yin girman kai don ya na da dukiya:

Idan ya dubi farkon sa, zai ga ba a haife shi da arziki ba, kuma ko da mahaifansa ma su arziki ne, ai wannan arziqin ba mallakarsa ba ne. Kuma ya kalli qarshen sa; ya tuna cewa idan ya mutu ba zai tafi da komai qabari ba sai likkafani. Idan kuma ya kalli al'ummar da ta shude da kuma wadda ya ke cikinta a yanzu zai ga cewa wadanda su ka fi shi suna da yawa. Idan kuma ya qara lura zai ga akwai waxanda sun yi dukiya kuma sun mutu ba tare da sun ci amfaninta ba, ko kuma suna raye amma Allah ya tafiyar da dukiyar, ko kuma ga dukiyar amma Allah ya jarrabe su da rashin lafiya wadda ta hana su jin dadin arziqin, ko fitinanninyar mace, ko fitinannun 'ya 'ya, ko barayi, ko abokan gaba, ko dinbin bashi da yake wuyansa, ko kuwa uwa-uba rashin kwanciyar hankali, musamman a yankunan mu na Afrika; mutum idan ya fita ba ya samun nutsuwa cewa zai koma gida lafiya; saboda tsoron ko dai a kashe shi, ko a sace shi, ko a yi ma sa fashi, ba don komai ba, sai don wannan dukiyar da yake da ita.

Kuma ya kalli misalin da Allah Madaukakin Sarki ya ba mu game da Qaruna, wanda ya yi dagawa da girman kai saboda tunanin ilminsa da gogewarsa a kasuwanci su su ka bashi wannan dukiyar ba Allah ba. Sai Allah Madaukakin Sarki ya sanya qasa ta hadiye shi. Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: (Qaruna) ya ce: “Haqiqa an bani (dukiyar) ne don wani ilimi da nake da shi.

Shin bai san cewa haqiqa Allah ya halakar da wadansu qarnunnuka da suke gabaninsa wadanda sun fi shi qarfi da kuma tara dukiya ba …" - (Suratul Kasas aya ta 78)

A qarshe sai Allah ya halakar da shi, kamar yadda ya fada ya ce:

“Sai muka shafe shi da gidansa a cikin qasa, ba shi da wasu jama'a da za su taimake shi koma bayan Allah, kuma ba ya cikin wadanda ake taimakawa." - (Suratul Kasas aya ta 81)

Wani misalin kuma shi ne yadda Allah Madaukakin Sarki ya aiko iska ta qone gonar wani mai gona da ya cika baki ya yi dagawa da girman kai ga dan uwansa, yana nuna ma sa cewa shi ya fi shi dukiya, amma Allah Madaukakin Sarki ya nuna ma sa cewa shi yake da iko akan dukiyar da yake taqama da ita. Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ya kasance yana da amfanin gona, sai ya cewa abokinsa, alhali yana mai jayayya da shi ya ce: "Ni na fi ka yawan dukiya da kuma buwaya ta vangaren mabiya". - (Suratul Kahafi aya ta 34).

Wannan mutumin Allah Madaukakin Sarki ya nuna ma sa shi ba komai ba ne, kuma iko da wannan gonar a hannun Allah yake, ya yin da Allah ya tura iska ta qone masa gonar, sai ga ta a zube akan saiwowinta. Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Sai aka zagaye ‘ya’yan itatuwan na sa (da wuta suka qone) sai ya wayi gari yana tafa hannayensa (daya akan daya, yana mai sallallami) a sakamakon abin da ya kashe akan gonar, alhali tana kwance akan saiwoyinta, yana cewa: “kaico na! Dama dai ban hada Ubangijina da kowa ba." kuma bai kasance yana da wasu jamaa da za su taimake shi ba koma bayan Allah, kuma bai kasance wanda ake taimakawa ba." - (Suratul Kahfi aya ta 43).

Haqiqa wadannan misalai sun ishi mai hankali daukan izina, ya kiyayi fushin Allah Subhanahu wa Taala, tun kafin ya hadu da shi, ko kuma ya lalatar da dukiyar da yake tunqaho da ita.

Sai mun hadu a fitowa ta 19 da yardar Allah

GIRMAN KAI KASHI NA SHABAKWAI

GIRMAN KAI KASHI NA SHABAKWAI

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 8:

Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?

Ci gaba...

2- Mataki na biyu: Jin tsoron Allah da ganin girmansa.

Duk mutumin da yake jin tsoron Allah da ganin girmansa ba zai siffantu da girman kai da ji-ji-da-kai da taqama ba, domin jin tsoron Allah da ganin girmansa, zai sanya ma sa ya riqa karvar gaskiya, kuma ba zai kasance mai wulaqanta mutane ba.

A nan mutum zai riqa qoqarin bin umarnin Allah da Manzon sa (saw) wajen yin abin da su ka yi umarni da shi. Duk wanda ya siffantu da haka kuwa, ba zai riqa wulqanta mutane ko ya daga mu su kai ko ya nuna mu su isa ba. Domin hadisi ya tabbata daga Iyadh bn Himar (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya yi mini wahayi akan ku riqa qan-qan da kai, har ya zamanto wani bai yi alfahari akan wani ba. kuma wani bai wuce gona da iri akan wani ba." - (Muslim: 7104).

Haka kuma mai girman kai, idan ya tuba ya luzumci tsoron Allah da ganin girmansa, kuma ya dubi kyakkyawar rayuwar managartan bayin Allah abar misali musamman jagoransu kuma shugabansu Annabi Muhammad (saw) zai san girman kai ba abin yi ba ne. Domin Manzon Allah (saw) duk da kasancewar sa sama da dukkanin halittun Allah a duniya da gobe qiyama, ya fi kowa qanqanda kai (saw).

Kaxan daga misalin tawadhu'unsa (saw) shi ne:

Hadisi ya tabbata daga sayyadina Umar da Abdullahi bn Abbas Allah ya qara yarda a gare su sun ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Ka da ku kambama ni kamar yadda Nasara (kirista) su ka kambama Annabi Isa an Maryam, ni bawan Allah ne don haka ku ce min bawan Allah kuma Manzonsa." (Bukari: 3189).

Haka nan an karbo daga Anas bn Malik (ra) ya ce: wata mace [mai tabin hankali] ta zo wajen Manzon Allah (saw) ya na cikin mutane ta ce ya ma'aikin Allah ina da Magana da kai, sai Manzon Allah (saw) ya ce: “Ya Babar wane! ki duba duk inda ki ke so mu zauna a cikin hanyoyin madina zan zauna na saurare ki" sai ta nemi wuri ta zauna kuma Manzon Allah (saw) ya zauna ya saurare ta har ta gama bayaninta". (Bukhari ya anbace shi Mu'allaqan hadisi na 6072, Muslim: 4293).

Haka nan an karbo daga Anas bn Malik (ra) ya ce: “Haqiqa Manzon Allah (saw) ya ga Majina a jikin bangon masallaci daga sai ya sa hannunsa mai albarka ya gogeta."

Haka nan an karbo daga Anas bn Malik (ra) ya ce: “Manzon Allah (saw) ya kasance ana gayyatarsa izuwa walimar da ba a tanadi komai a cikinta ba sai gurasar sha'ir da kakiden da ya fara bashi da fumfuna kuma ya amsa gayyatar, kuma haqiqa ya bayar da jinginar sulkensa ga wani bayahude ya karbi abinci, bai samu ya biya ba har ya koma ga Allah." (Musnad u Abu Ya'ala al mausuli, hadisi (3904)

Har ila yau an karbo wani hadisi daga Anas bn Malik (ra) ya ce: "Babu wanda ya fi soyuwa a wajensu kamar Manzon Allah (saw). Ya ce sun kasance idan su ka ganshi ba sa miqewa tsaye saboda sun san ba ya son haka." (Adabul Mufrad: 946. Da sunan at-Tirmizi: 2754).

Qanqan da kansa (saw) bai tsaya ga nan ba. Barima Manzon Allah (saw) ya kasance yana taya iyalansa ayyukan gida, yana cin abinci tare da sahabbansa, yana zama tare da talakawa yana shiga kasuwa don yin ciniki ko siyayya.

Hadisi ya tabbata daga Aswad Bin Yazid (ra) ya ce: Na tambayi Nana A'ishah (R.A), Me Manzon Allah (saw) ya kasance yana yi a cikin gidansa? Sai ta ce: “Ya kasance yana taya iyalansa aiyukan gida. Idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah." - (Bukhari: 676).

Kuma hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (ra), ya ce: Manzon Allah (saw) yace: “Babu wani Annabi da Allah ya aiko face ya yi kiwon dabbobi." Sai sahabbansa suka ce: “kai ma kayi?” Sai ya ce: “Na'am! Na kasance ina kiwon dabbobi ga mutanen Makka, su na biya na wasu ‘yan sululluka.” - (Bukhari: 2262).

A wani hadisin kuma daga Abu Hurairah (ra) har ila yau ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Idan da za a gayyace ni walima wadda za a yi da qwaurin dabba zan amsa (gayyatar), kuma idan da za a yi mini kyautar qwaurin dabba zan amsa.” - (Bukhari: 2568).

Babban sahabin nan, kuma hadimin Manzon Allah (saw) , Anas dan Malik (ra) ya ce: “Haqiqa shi ya wuce yara, sai ya yi mu su sallama, sai ya ce: (na yi haka ne don) Manzon Allah ya kasance yana aikata hakan." - (Bukhari: 6247)

Duk wadannan hadisai da mu ka ambata, da sauransu, su na nuna mana tawadu'un sa (saw) duk da kasancewar fiyayyen halitta. To ina kuma ga wanda ya ke ba kowa ba ba annabi ba kuma Manzo ba? Lallai wannan shi ya fi kamata ya zama mai qanqan da kai domin koyi da fiyayyen halitta Annabinmu Muhammad (saw). Allah ka sa mu dace, amin.

Sai mun hadu a fitowa ta 18 da yardar Allah.

Saturday, 7 November 2015

GIRMAN KAI KASHI NA SHA SHIDA

GIRMAN KAI KASHI NA SHA SHIDA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 8:

Waxanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?

AMSA:

Haqiqa hanyoyin magance wadannan cututtuka sun danganci abin da ya sabbabawa mai su dabi'antuwa da su. Matakan da za su taimakawa wajen rabuwa da su su ne kamar haka:

1- Mataki na farko: Mutum ya san iyakacin kansa da kuma gazawarsa.

A nan mutum mai girman kai zai kalli kansa a matsayinsa na xan Adam, wanda a da babu shi, sai Allah ya samar da shi, kuma ya tsara halittar sa a yadda ya ga dama, kuma ya ba shi daga abin da ya so, kuma a qarshe zai mutu babu makawa. Mutum zai kalli gazawarsa a matsyinsa na dan Adam mai gangar jiki wanda ba ya iya rayuwa sai ta hanyar numfashi da Allah ya hore ma sa da ci abinci da sha da yin bawali da bayan gida. Kuma cuta tana iya samun sa a lokacin da ba ya so. Sannan ya dubi gazawar sa ta bangaren gani da ji da sauran al'amura da yake da su kamar qarfi da mulki da kuma dukiya. Idan ya kalli wadannan da idon basira zai ga dukkaninsu taqaitattu ne.

A gefe guda kuma sai ya dubi girman Allah da isar sa da qasaitar sa da mulkinSa da yadda komai yake qarqashin ikonSa, da yadda ya tabar da ma su girman kan da su ka gabace shi da makamantansu ba tare da sun gagare shi ba.

Kamar Adawa da Samudawa da Fir'auna da Qaruna da sauran dagutai ma su girman kai a ban qasa.

Wannan zai sanya mai girman kai ya gane cewa shi ba komai ba ne, wadanda su ka fi shi ma sun gama tunqahon su, Allah ya yi maganinsu, saboda duniya budurwar wawa ce. Wannan zai qara nuna ma sa cewa girman kai da ji-ji-da-kai ba su cancance shi ba.

Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Shin lokaci bai zo wa dan Adam ba, wanda ya kasance ba komai ba ne? Haqiqa Mu Mun halicci dan Adam daga digon maniyyi kwababbe (maniyin namiji da qwan mace), sai mu ka sanya shi ya zaman to mai ji, da gani." - (Suratul Insan 1-2)

Wannan ayar ta nuna yadda dan Adam ya kasance a matsayin babu shi a wani lokaci a baya, amma aka samar da shi daga digon maniyyi, sannan kuma aka sanya ma sa ji da gani da lafiya, kuma kamar haka ne wata rana zai zamanto babu shi, kuma duk abin da yake taqama da shi zai iya rasa shi, ko ya mutu ya bar shi, kuma zai koma ga Allah Madaukakin Sarki ya sami sakamakon abin da ya aikata.

Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Sannan Allah zai matar da shi sai a bunne shi, sannan zai tashe shi a lokacin da ya so." - (suratu Abasa, aya ta 21-22)

Sai mun hadu a fitowa ta 17 da yardar Allah.