Monday, 2 June 2014

hmmmmmmmmmmmmm

Hahahahahahhh.Ba kano sarkin dabara.

Wani bakano ne sukayi gaddama shida wani bakatsine.

Bakano yace da bakatsine ni nafika dabara bakatsine yace a a bakano ni nafika dabara.... Suna cikin musu sai bakano yace to kai dabarar taka guda nawace? Sai bakatsine yace ni dabarata guda dayace. Sai bakano yace to ni dabarata dari badaya (99) sai bakatsine to shikenan.

Wata da daddare sai suka tafi wani gidan gona abaya gari suka shiga tawata yar qaramar qofa domin an kulle babbar kofar. Suna shiga sai suka tarar da soyayyen nama

da zuma. Nanfa suka fara cin nama suna shan ruwan zuma. To shi bakatsine idan yacinama-yacinama sai yaji qofar yajaraba fita. Domin yasan idan cikinshi yacika da nama bazai iya wucewa taqaramar kofar nanba. Shikuwa bakano yasaki tunbi yadinga diban nama da zuma har saida cikinshi yayi kamar yafashe.

Zuwacan da gari yakusa wayewa saisukace yakamata mutafi domin kar gari yawaye masu gona sutarar dasu. to dasuka fita sai batsine yafara ququtawa yafita daqyar. shikuwa bakano yayi-yayi yakasa fita domin yacika tinbinshi danama da zuma. Sai bakatsine yace dashi to waikai ina dabarun naka suke? Sai bakano yace aiduk nagama quresu. Sai bakatsine yace to nizan aramaka tawa dabarar sai bakano yace to. Saibakatsine yace idan kaji masu gona sunkusan zuwa ka kwanta kayi shiru kamar kamutu yace to. Bakatsine yatafi yabar bakano.

Masu gona nazuwa suka bude qofa suka shiga saiga mutun akwance kamar yamutu. Kawai sai sai babban cikinsu yafara cewa Allah sarki kaga wani bakano yaci nama yayi mishi yawa har yamutu. Sai sukayi kama-kama suka dauko shi suka ajiyeshi awaje sai suka koma cikin domin suga irin barnar dayayi. Suna shiga sai banao yatashi yakintuma aguje jikake duf-duf-duf. Hahahahahahah Wuta salau.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: