Tuesday, 24 June 2014

Wasanni

WASANNI: Brazil Ta Lallasa Kamaru Da Ci 4-1 Brazil ta tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa Kamaru da ci 4-1 yayin da Mexico ta doke Croatia 3-1 duka a rukunin A. Dan wasan Barcelona Neymar ne ya fara zira kwallo a minti na 17 kafin Joel Matip yafarke wa Kamaru a minti na 26. Neymar ya sake zira kwallo ta biyu a minti na 34 kafin Fred ya zira ta uku da ka tare da taimakon David Luiz sannan Fernandinho ya zira ta hudu ana dab da tashi.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: