Wednesday, 29 October 2014

ALLURA FAH

ABU 4 SUNA CUTAR DA JIKI
1- yawan magana
2- yawan barci
3- yawan jima'i
4- yawan cin abinci

ABU 4 YANA RUGUZA JIKI
1- bakin ciki
2- bacin rai
3- rashin barci
4- yunwa

ABU 4 YANA JANYO ARZIKI
1- yawan istigfari
2- tsayuwar dare
3- yawan sadaka
4- Zikirin safiya da yammaci (irin wanda Annabi SAW ya koyar)

ABU 4 YANA HANA ARZIKI
1- baccin asuba
2- karancin sallah
3- kasala
4- Ha'inci

ABU 4 YANA BUSAR DA FUSKA DA TAFIYAR DA HASKENTA
1- karya
2- bushewar zuciya
3- yawan tambaya ba akan ilimi ba
4- yawaita fajirci

ABU 4 YANA KARA HASKEN FUSKA
1- tsoron Allah
2- cika alkawari
3- yawan kyauta
4- kame kai
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: