v Rana ce da ALLAH yayi rantuwa da ita “ina RANTUWA da alfijir da darare goma “[fajr 1-2] wasu daga cikn malaman Tafsiri sun tafi akan cewa alfijir din ranar arfa ALLAH yayi rantuwa da shi.#
v Ranar da addini ya kamala kuma aka cika mana ni’ima. ALLAH Ta’ala yace “a Yau na Kammala Muku Addininku kuma na cika ni’imata Akanku Kuma Nayadar muku A musulunci A matayin addini [MAIDA 3] #
v Ranar Al’ummar Musulmi n Duniya Suke Taruwa Domin Bautawa ALLAH Da kuma Gode Masa Tare Da Bayana Farin Ciki. Manzon Allah [SAW] Yace “ranar Arfa Da Ranar Sallah Baba da Kwanaki Yanyane [Aiyamut Tashrik] Idin Mune Mu Ma’abota Musulunci Da kuma Nuna Farin Ciki ‘’ [Abu dauda ya rawaito].#
v Azumin Ranar Arfa yana kankare zunban shekara biyu [2] manzon allah [SAW] yace “Azumin Ranar arfa idan kayi shi sabo da allah yana kankare Zunubin Shakarar da tagabata da kuma mai zuwa [Musulimu ne ya rawaito] Don Haaka An son Yin Azumin ga Wada Baije Haji Ba, Amma wanda yaje hajji zaifi kyau ya himmatu wajen yin aikinsa na hajji.#
Ranar Arfa Itace Ranar Da Allah Yake Alfahari Da Bayinsa Lokacin Da Zaice Da Malikun sa “yaku Malaikuna Kuyi Duba Izuwa Ga Bayina Hakika sunzo Gareni Fururu Gasu Cikin Hantsi’’ [Ibn Hibban Ya Rawaito] Ibn abdul Barri Yace ‘’Wannan Hadisi yana nuna cewa Angafarta Musu, Domin ALLAH Baya Afahari Da Masu Barna Har Sai sun Tuba An Gafarta Musu. Manzon [SAW] Yace ‘’Mafificiyar Addu’a A Ranar Arfa Da Kuma Mafificin Abinda Na Fada da Annabawa Da suka Gabaceni Shine#
LA’ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLU SHAI’IN KADIR.
Bukhari da muslim kuma tirmizi ma ya rawaitoshi
ALLAH YABAMU IKON YINSA AMEEEEEEEEEEEN SUMA AMEEEEEEEEEEEEEEEEN

0 comments: