Monday, 3 November 2014

Gyara Kayanka:

Hakika muna cikin wani irin jarabawa mai tsananin gaske cikin wannan Kasa tamu Nigeria; muna cikin jarabawar rashin mulkin adalci daga wasu shugabanni, muna cikin jarabawar yaduwar cututtuka daban-daban, Muna cikin jarabawar fadace-fadace irin na kabilanci da addini, muna cikin jarabawar yan fashi da makami, muna cikin jarabawwar masu daukan makamai domin yakar talakawa da hukuma.



Hakika, wadannan bala'o'i da muka ambata sun yi sanadiyyar tabarbarewar al'amura, sun yi sanadiyyar yaduwar talauci da rashin aikin yi tskanin yan kasa, sannan uwa-uba sun yi sanadiyyar kashe rayukan jama'a da yawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba. "Fa inna lillahi wa inna ilaihi raaji'un"



Annabi s.a.w yace "Alfahsha bata taba bayyana a cikin wasu mutane har sukai ado da ita ba face annoba ta watsu acikinsu da (ciwuka) Cututtukan da basu taba ganin
irinsuba, basu kuma taba tauye mudu da sikeli ba face an kama su da tsananin fari, da kuncin rayuwa da zaluncin shugaba, basu taba hana zakkah ba face
an hanasu ruwan sama badon dabbobi ba ma da kwata kwata ba ayi musu ruwaba, basu taba warware alkawarin Allah ba da alkawarin manzonsa face Allah ya dora makiyinsu akansu, makiyan suke dauke da sashen abunda suka mallaka, matikar shuwagabanninsu basuyi hukunci dahukuncin Allah ba sai Allah ya sanya tsanani a tsakaninsu".Ibn Majah 4019 da ihya kutub al'arabiyah.



Annabi s.a.w. Yace "idan kukai kasuwanci irin na ruwa, kuka riki bindinan shanu,kuka amince da hatsi ( ma'ana kuka karkata zuwaga holewa rayuwa), kukabar jihadi, to Allah zai buga kaskanci akanku bazai cireshi ba har sai kun komazuwaga (cikakken) addininku" sunan Abidawud 3462 maktabatul asriyyah,hadisine sahihi.



Yan'uwa Musulmi! Lalle in muka dubi wadannan hadisai da kuma halin da mukatsinci kanmu, Sai muce Annabin mu s.a.w yayi gaskiya. Dama mai gaskiyane abun gaskatawa. Amma duk da wannan hali da muke ciki na tabarbarewar lamura
ba za mu fidda tsammanin kyautatuwar Wadannan lamuran ba, ba za mu fidda
tsammanin samun rahamar Allah da tausayinsa gare mu ba. Saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce cikin suratul Hijri aya ta 56: ((Babu mai yanke tsammanin
samun rahamar UbangijinSa sai batattu)).



Ya kuma cewa a cikin suratul A'araafi aya ta 156: ((Rahamata ta yalwaci dukkan kome, da sannu zan rubuta ta ga wadannan da suke tsare dokokin Allah suke ba da zakka, watau wadannan da suke imani da ayoyinmu)).



Yan'uwa Musulmi! Da ma ita rayuwar mutum haka take, wata rana cikin dadi, wata Rana kuwa cikin wahala, to amma su al'ummar Musulmi wadanda suka yi
imani da Allah a matsayin Ubangijinsu, suka yi imani da Musulunci a matsayin addininsu, suka yi imani da Muhammad (saw) a matsayin annabinsu kuma Manzo zuwa gare su, lalle wadannan ba sa gushewa cikin alheri bayan alheri matukar dai
zukatansu na rataye da Ubangijinsu, suna kuma kaskantar da kai gare Shi suna kuma nuna naciya cikin rokon Shi dare da rana.



'Yan'uwa Musulmi! Lalle abu mafi alheri da al'ummar Musulmin Nigeria za su aikata domin samun kubuta daga bala'o'in da suke cikinsu yanzu, shi ne mura'ja'ar kai, da kyautata ayyuka, da kuma fiskantar Allah Madaukakin Sarki cikin kaskantar da kai, da kuma yawaita addu'a dare da rana; saboda ita addu'a wani babban makami ne ga salihan bayi, a gaskiya ma addu'a ita ce ginshikin ibada.



Abu Dawud cikin hadisi na 1479, da Tirmizi cikin hadisi na 2969, da Ibnu Majah cikin hadisi na 3828 sun ruwaito da isnadi sahihi daga Nu'uman Dan Bashir cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Addu'a ita ce Ibadah)) daga
nan sai ya karanta fadar Allah cikin suratu Gafir aya ta 60: {Ubangijinku Ya ce ku roke ni zan amsa muku, lalle wadanda suke nuna girman kai ga bauta mini da
sannu za su shiga Jahannama suna kaskantattu}.


Allah nake roko da ya yaye mana wadannan cututtuka ya kuma kawomana zaman lfy da kwanciyar hankali a kasar mu da sauran kasashen musulmi. Ameen.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: