Monday, 24 November 2014

MUSULUNCI HASKENE TARIHIN WANI MUTUM MAI TONON KABARI

MUSULUNCI HASKENE
TARIHIN WANI MUTUM MAI TONON
KABARI

""karanta kasha mamaki""

Wata rana wani mutum yazo
wurin (Sayyidina Ali Bin Abi
Talib (r.t.a) sai yace ya amirul
muminina nazo ne domin in tuba
daga laifukana sai sayyidina Ali
yace wadanne laifuka kenan?
Sai mutumin yace ni nakasance
ina tonon kaburburan bayin Allah
bayan an binnesu, to sai naje
jana'izar wata gawa kuma an
binneta tare dani.

Bayan an watse sai nakoma
domin in tone kabarinta, ina bude
kabarinta kenan sai Allah ya ba
gawar nan ikon magana, sai tace
min

"KAICONKA BAKA JIN KUNYAR
ALLAH"? KAZO KA TONE KABARINA
KA KETA SIRRINA A TSAKANIN
MATATTU, GASHI KAI AN GAFARTA
MAKA ZUNUBANKA"

sai mutumin yace wane aiki nayi
wanda Allah ya gafarta min? Sai
tace saboda ka sallaci gawata
(sunnah ta tabbatar da cewa duk
wanda ya sallaci gawar mumini to
an gafarta masa laifukansa)
sai yace mata don Allah ki tsaya
zan tambayeki wadansu
abubuwa sai tace to kada ka
tsawaita Sai yace yayin da nake
bincike a cikin
kaburburan mutane naga
wadansu mutane fuskokin su
basu dubin gabas (dama kowa
idan za a sa shi a kabari fuskarshi
gabas take kallo), kuma naga
wasu mutane tsirara babu
likafani a jikinsu a cikin
kaburburan su, kuma naga wasu
mutane likafani ne kawai babu
jikinsu.

Sai gawar tace ma mutumin lallai
kayi gaskiya, mutanen da kagani
fuskokinsu basu dubin gabas
sune masu shan giya, mutanen da
ka gani babu likkafani a jikinsu
sune wadanda suke haduwa
suna wanka tsirara kowa na
ganin al'aurar kowa (Annabi s.a.w
yace Allah ya tsinewa mai dubin
al'aurar wani da kuma wanda
akayi duban zuwa gareshi), su
kuma wadanda kaga likkafani
kawai babu jikinsu sune masu
aiki irin na mutanen annabi ludu
(luwadi) lokacin da aka sa su a
cikin kabarinsu sai mala'iku su
daukesu su kaisu inda aka
halakarda mutanen annabi ludu
ana azabtar dasu tare dasu har
ranar alqiyama....

sai gawar tace rufeni ka
mayarmin da kasata. Sai mutumin
yacema sayyidna Ali wannan
shine karshen abinda ya faru
atsakanina da gawar.

sai sayydina Aliyu yace in kayi aiki
da tubar ka kuma kai tuba mai
kyau ba tuban muzuru ba.


Ya Allah muna rokonka da
sunayenka kyawawa:
Allah ka
tsaremu daga wannan
mummunan aiki. Allah ka shiryi
zuri'ar musulmai, Allah ka yafe
mana zunubanmu dan darajar
Annabin da babu wani bayanshi.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: