YIN KUKA SABODA TSORON ALLAH.
Abu Huraira Allah ya yarda dashi ya ruwaito daga Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace:
"Duk wadda yayi KUKA saboda Tsoron Allah, bazai shiga wuta ba har sai in za'a iya mayar da Nono cikin hantsarsa, Ma'ana (inda aka tatso shi nonon)."
[TIRMITHI]
Shin kuwa haka zai
yiwu A mayar da
nono jikin dabba
(hantsa) bayan an
tatsoshi tuntini ???
Wannan ba abune wadda zai yiwuba.
Toh haka nan duk
mutumin da yayi Kuka kawai saboda
jin tsoron Allah, babu abinda zai hana masa shiga Aljannah, inji Annabi (s.a.w).
Yan uwa, mu rinka nazari tareda ganin Ayoyi da Halittun Allah Ta'ala wadda zasu
kara mana karfin Imani.
Ya Allah! Kakara mana Imani, kabamu ikon Nazartar halittu da ayoyinka, domin Idonmu su zubar da hawaye don tsoronka kuma musamu falalar Shiga Aljannah.
YIN KUKA SABODA TSORON ALLAH.
Tags:
fadakarwa

0 comments: