Friday, 5 December 2014

WAKAR NIGERIA HAHAHAHA

WAQAR NIGERIA

TA BASHIR MUSA LIMAN

Sakamakon halin da Najeriya ta kasance a ciki, sai na yi nazari hade da fito da hanyar da komai zai daidaita, a samu zaman lafiya a kasa. Waka ce da ta bayyana matsalolin da suka yi cacukwi da kwalar Najeriya har suke neman farraka ta. Ina fata za a yi nazarin wakar
don a samun romon darussan da take koyarwa. A sha karatu lafiya:

1 Godiya ga Jallah Sarki daya,
Da ake bauta masa Shi daya,
Shi Ya haskaka rana a duniya,
Taimake ni a wakar Najeriya.

2 Salati dubu ga Angon Aisha,
Wanda ya hana aikata alfasha,
Kaki bin sa ka zama shashasha,
A karshe ka yi kuka da idaniya.

3 A yanzu na kasance cikin kunci,
Idanuna na zafi sun gaza barci,
Zuciyata kuwa cike da takaici,
Da na kalli kasata Najeriya.

4 Abubuwa sun sukurkuce,
Tabbas al’amura sun rikice,
Najeriya kuwa ta balbalce,
Ya Ubangiji ceci Najeriya.

5 Yanzu gani ina cikin kuka,
Rayuka na salwanta babu iyaka,
Saboda tashin bam babu iyaka,
Haka za a ci gaba a Najeriya?

6 Shugabanni kamar almajirai,
Sun maida‘yan Naija sakarkarai?
Kuma tabbas duk sun sani sarai,
Suna ta walawa da kwalliya.

7 Yanzu Arewa ta koma baya,
Tattalin arziki ya samu karaya,
Shugabanninta sun juya baya,
Ga taruka amma babu matsaya.

8 Cacai da baki suna furtawa,
Hanyoyin da zai magantawa,
Amma sun kasa aiwatarwa,
Sun koma gefe suna dariya.

9 Al’amarin gobara daga kogi,
Shugabanni sun shiga sabgogi,
Sai tarukan banza da na bogi,
To ko yaushe za a yi dariya?

10 Wadatar zuciya, tafi dukiya,
Farin cikin zuciya, yafi dukiya,
Ramuwar gayya baya sa dariya,
Zaman lafiya, yafi zama sarauniya.

11 Zuciyata ta shiga harbawa,
Idanuna sun yi ja har da kadawa,
kwakwalwata ta shiga sarawa,
Ina ta gudu, ina ta hada hanya.

12 Idan na tuna sai na ji hawaye,
Annunshuwa da murna sun yaye,
Tafiya ta yi tafiya babu tsimaye,
Abubuwa za su daidaita a Najeriya?

13 Yanzu ana barci da ido daya,
Gudun kada a aikata maka tsiya,
An kasa zama tsintsiya guda daya,
Hakan ya sanya Turawa dariya.

14 Ka shiga mota za ka yi tafiya,
Ga jami’an tsaro sun cika hanya,
Rike da bindiga suna zare idaniya,
Sai su yi harbi su kuma yi dariya.

15 Masu babura suna yin turi,
Wai da babura ake kaiwa hari,
Duk da hakan ana kaiwa hari,
Hakan zalunci ko kin gaskiya?

16 Gwamnati ta ce ai tattaunawa,
Boko Haram sun zam amincewa,
karshe aka sharar da sulhuntawa,
Anya ana so a yi zaman lafiya?

17 Boko Haram za ta zam bacewa,
Inji Jonathan ko me ya yi takawa?
Yanzu ga hare-hare na ta karuwa,
Shugaba ne ko karan-kada-miya?

18 A yanzu hankali a tashe yake,
Ta ko’ina ka duba a tsaye ake,
Idanun mutane kalle-kalle suke,
Kasancewar kasa ba zama lafiya.

19 Ba ta wutar lantarki ake yi ba,
Ko ruwan sha mai sanyi ake yi ba,
Ko a samu hanyoyin motoci ba,
Kai dai a samu zaman lafiya.

20 Mai cin kasa kiyayi ta shuri,
A daba wuka a ciki ana kirari,
Tabbas abubuwa ba sa cikin tsari,
Ana ta yin kwan-gaba-kwan-baya.

21 Idan na kalli wannan duniya,
Samanta rufe yake da samaniya,
Ciki har da babban kogin maliya,
An bata komai don rashin gaskiya.

22 Bakuna sun zam rabuwa,
Kan yadda za ai shawowa,
Matsalar da ta-ki-cinyewa,
Wayyo Allah! kasata Najeriya.

23 Cin hanci har da rashawa
Ka yi aiki har da gamawa
Kudin fansho an hanawa
Har mutuwa babu naira daya

24 Jaridu ku tsayar da gaskiya,
Kada ku ba da labarin waskiya,
Ko ku rika goyon bayan karya,
Kullum ku rika watsa gaskiya.

25 Amurka mai fada da ta’addanci,
Har yanzu tana cikin halin firgici,
Kasancewar ba ta samun sassauci,
Sai ma barci take yi da ido daya.

26 Kada ta zuga ‘yan Najeriya,
Har su tsokalo babbar zuliya-
Ta dodo mai tsananin karfin tsiya,
A karshe a yi ta kuka da idaniya.

27 ‘Yan Kudu suna kira a raba kasa,
Domin Arewa ba ta bunkasa kasa,
‘Yan Arewa sun ki yarda a raba kasa,
Sai sharar gara suna sheka dariya.

28 Jama’a a koma ga Allah,
A tsayar da azumi da Sallah,
Da yin nafila don samun falalah,
Allah Zai bada zaman lafiya.

29 Tawassali da Annabin karshe,
Mai kyawun fata har da harshe,
Mai furta kalamai a tausashe,
Allah Ya kawo mana zama lafiya.

30 Bashirun jaridar Aminiya,
Da ya je Kano har da Zariya,
Yayan Ahmad da Shamsiyya,
‘Yan Najeriya a zauna lafiya.

31 Tammat a nan zan sa aya,
A waka mai baiti talatin da daya,
Wadda take kira a zauna lafiya,
Cikin shekarar 2012 aka shirya.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: