Wednesday, 8 April 2015

Labarin Tsohuwa Da soja

Wata tsohuwa ta zo Kusa da road block na sojoji zata tsalaka
titi, sai wani daga cikin sojojin ya tsallakar da ita.
Tsohuwa taji dadi sosai tayi mai addu'a kamar haka;
Tsohuwa: Nagode, Allah ya baka Commanda.
Soja: Amin.
Tsohuwa: Allah ya kareka.
Soja: Amin.
Tsohuwa: Allah ya albarkaci abunda kake samu.
Soja: Amin.
Tsohuwa: Allah ya baka mata takwarai.
Soja: Amin.
Tsohuwa: Allah yasa a turaka Maiduguri ka taimaki yan uwan
mu.
Soja: Tsohuwa zanci ubanki kenan wallahi!!
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: