. A wannan lokaci ne kafin Annabi Muhammad (SAW) ya kai shekaru uku wannan abin mamaki ya faru, ance Muhammad (SAW) yana wasane a cikin yanki, a bayan wani zango na kabilar Halima yaronta wanda ya ruga ya ambata mata abinda ya faru, kamar haka labarin ya zo da shi. . Imam Muslim (RA) ya ruwaito shi ta wajen Anas dan Malik (RA) da cewa: ‚Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, mala’ika Jibrilu ya zo mashi lokacin da ke wasa da yara, ya kama shi ya kayar da shi, ya tsaga kirjinsa, ya fitar da zuciyar (sa) kuma ya fitar da wani gudan jinni, sai (Jibrilu) ya ce, ‚wannan wani rabo ne na shaidan aka cire maka shi,‛ sa’an nan ya wanke shi (zuciyar) da ruwan zamzam a cikin wata tasa na zinare’ sa’an nan ya mayar ya dinke, kuma ya mayar da shi in da yake,‛ sai yara suka ruga da gudu zuwa ga uwarshi (ta goyo) su ka ce, ‚Lallai Muhammad an kasheshi,‛ sai jama’arsu suka doshi in da ya ke suka iske shi har launinsa ya canza.‛ Anas dan Malik ya ce, ‚na kasance ina ganin alamar jini a kirjinsa (SAW).‛ Sahih Muslim Fassarar Hausa (1/135) 1993 wannan tarihi masana tarihi irinsu dan Is’hak ya gargadi jama’a cewa, zuwan mala’ika da tsaga kirji ba shine dalilin komawar Muhammad (SAW) zuwa ga iyayensa ba, don masana sunce Halima ta ambaci labarin cewa, wasu kiristocin Itofiya suka nemi daukar shi Muhammad (SAW) da dabaran wai zasu kaishi can don yana da wata alamar daukaka tare da shi. . Ga maganarsu kamar yanda Halima ta ambata cewa sun ce: ‚Bari mu dauki wannan yaro zuwa kasarmu muba sarkinmu don mun fahimci wani abu zai faru da shi,‛ don haka Halima ta gudu da shi don kare lafiyarsa wannan labari kuma dabari ya amabce shi tare da nuna rashin yardan sa da wannan labari, don haka masana da gabashiyar duniya (mustari}ai wanda ake kira da suna, (‘Orientalists’) da wasu musulmai basu gaskata wannan labara ba. Saboda shekarunsa na zama da kabilar Banu Sa’ad a shekaru na biyar ne ba uku ba. Kuma saboda haka ne Halima ta mayar da shi zuwa ga uwarsa haka ya kara sanya wasu masana tarihi rudani. . Kuma kawo labarin Mr William Muir na karawa tarihin Muhammad (SAW) tsari a bangarori masu yawa. Saboda haka ba kowa ya ke sanin cewa, idan labari bai inganta ba daga Annabi (SAW) ba dole ne a yarda da shi ba. Saboda haka wasu ke fassara suratul Sharhi ta sauka ne don kara goyon bayan tsaga kirji daga cikinsu akwai Imam Ahmad ya ruwaito wanda ke cikin Tafsirin Ibnu Kathir ta wajen Abuhuraira a karkashin fassarar sura bisa fadar Allah Madaukaki cewa: . ‚Ashe, ba Mu buda maka zuciyarka ba (domin daukar hakuri da fahimta). Kuma Muka sarayar maka da nauyinka (94:1-2).‛ . Wannan sura na karantarwa da tabbacin buda kirgin wani abu daga Allah ko da yake ba tana nufin tsagawa face haskaka mashi zuciya wanda hadisin tsaga kirji ya gabata wanda aka samo ta wajen Abuhuraira da littafin Sahih Muslim. Maganar masana na gabacin duniya ba shi da wani tasiri a ko da yaushe don suna dogara ne da tarihin da bai tabbata ba kuma labarin abokan gaban Musulunci suka fi bayyanawa kuma su kafirai ne.
Bayani A Kan Tsaka Kirjin Ma'aiki (S.A.W)
Tags:
Tarihin Magabata

0 comments: