Saturday, 7 November 2015

GIRMAN KAI KASHI NA SHABIYAR

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 6:

Wane irin narko Ubangiji (swt) ya tanadawa ma su girman kai da ji-ji-da-kai da nuna taqama?

Ci gaba...

B) Uqubar da Allah ya ke yi wa masu girman kai a ranar lahira.

i) Allah yana wulaqantar da ma su girman kai a ranar Al-qiyama, domin hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Za a tashi ma su girman kai da ma su taqama ranar alqiyama, an mayar da halittarsu kamar qwayar komaiya, mutane su na tattaka su, saboda qasqancin su a gurin Allah.”

(Attawadu'u wal khumul na Ibn Abiddunya, Hadisi na 225)

ii) Qarshen makomar mai girman kai ita ce wuta:

Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Lallai wadanda su ke girman kai ga barin bauta mini da sannu za su shiga Jahannama su na qasqantattu." - (Suratul Gafir aya ta 60).

A wata ayar kuma, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Za a ce: ku shiga qofofin Jahannama kuna ma su dauwama a cikinta. Tir da mazaunin masu girman kai.” - (Suratul Zummar aya ta 72).

Kuma hadisi ya tabbata daga Abdullahi Bin Mas’ud (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda a zuciyarsa akwai girman kai gwargwadon qwayar komaiya, ba zai shiga Al-Jannah ba.” - (Sahihu Muslim: 91).

Kuma hadisi ya tabbata daga Abdullahi Bin Amr (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda ya kasance akwai girman kai gwargwadon qwayar komaiya a zuciyarsa, Allah zai kifa shi akan fuskarsa a cikin wuta.” (Musnad Ahmad: 7015).

Wani hadisin kuma ya inganta daga Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saw) ya ce: Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Jin girma mayafi na ne. Jin qasaita kwarjalle na ne. Duk wanda ya ja da ni a cikin daya daga cikinsu, zan jefa shi wuta." - (Sunan Abu Dawud:3567, Sunan Ibn Majah: 4164).

TAMBAYA TA 7:

Mene ne matsayi da kuma sakamakon da masu qanqan da kai su ke samu a gurin Allah?

AMSA:

Haqiqa hadisi ya tabbata daga Sauban (ra) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda ransa ya bar gangar jikinsa (ya mutu), yana kubutacce daga abubuwa uku (3), zai shiga Al-Jannah; Girman kai da bashi (Ana nufin mai taurin bashi wanda ba shi da niyyar biya) da cin dukiyar baitul mali." - (musnad Ahmad: 22369. Sheikh Shuaib al-Arna'ux ya inganta shi).

A wani hadisin kuma Abu Hurairah (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Sadaka bata taba rage dukiya ba, kuma Allah bai taba qarawa bawansa mai yin afuwa ba sai buwaya, kuma ba wanda ya taba qanqan da kansa (tawalu'u) a cikinku face Allah ya daukaka shi." (Muslim: 4689).

Sai mun hadu a fitowa ta 16 da yardar Allah.

Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: