TSOHON ALKALI.
Sheik Abubakar Muhamud Gumi (Rahimahullah)
A rayuwar malam an taba tambayarshi wata Shari'ace wacce kayi tafi baka mamaki ko bazakataba mantawa da ita ba???
Sai malam yace, akwai wata shari'a dana tabayi da tafi bani mamaki wanda bazan manta da ita ba,,,
Malam yacigaba da cewa, A wani gari akwai wan Attajiri da yake kasuwanci tare da wani mutumi amma bawanda yasan kudin ko nawaye a cikinsu, mutane na tsammani ko kudin nasune su biyu suka hada hannun jari suke kasuwanci...
Ananan haka, sai wata rana ciwon ajali ya kama wannan Attaji, da yaga ba halin tashi sai ya tara iyalansa da yan uwansa da wasu mutane na daban yace,"idan na mutu dukiyar dake hannun Alhaji wane tawace ni kadai baida ko sisi ciki." bayan nan wannan Attajiri sai ya mutu...
Bayan mutuwarsa sai akajewa da wannan dan uwan kasuwancin nasa da wasiyar wannan Attajiri, akace Alhaji yace idan ya mutu asa dukiyar dake hannunka a gado domin tashice shi kadai. koda yaji haka sai ya tunbatse yace Alhaji karya yake wannan dukiya tawace ni kadai baida ko kobo ciki, kawai dai na jashi a jikine muna kasuwanci tare don ya samu wani abu...
ABU KAMAR WASA... rigima har kotu akaita rafka shari'a har Alhaji mai rai yace aje Maqabarta a tambayi Alhaji mai mutuwa dukiyar waye zai fadi kota waye,, yan uwan Alhj mai mutuwa suka yarda abd sunsan ba'a mutuwa a dawo ballantana na kabari yayi magana,,, nan take aka rankaya da alkali da lauyoyi da Alhj mai rai da yan uwan Alhj mai mutuwa aka nufi maqabarta da akaje Alkali ya kira sunan Alhj mai mutuwa bisa mamaki sai akaji muryansa ya amsa, Alkali yace dukiyar daka mutu ka bari ta waye?? Alhj mai mutuwa tace ta Alhj wanene ba tawa ba.... wannan abu ya tsorata wannan alkali harya rasa yadda zaiyi gadai mamaci yayi magana abinda baiko tabaji a wannan zamani ba...
Ananan sai akaji labarin wani babban Alkali Sheckh Abubakar Muhamud Gumi a garin Kaduna a lokacinsa ba Alkali irinsa,, nan take akazo aka fada masa duk yadda abin ya faru tundaga mutuwar Alhj har maganar da yayi a kabari, Malam naji ance mamaci yayi magana sai yace karyane wanda ya mutu baya magana yace amma muje naji da kunnena.... yabisu har can garin akaje makabartan da Alhj ke kwance aka nunawa Malam kabarin Alhj, Malam ya kira sunan Alhji yaji Alhj ya amsa, yace dukiyar daka mutu ka bari ta waye??? Alhj yace ba tawa bace ta Alhj wanene (ya fadi sunan Alhj mai rai)... (Wannan abu ya daurewa Malam kai ace mutum ya mutu yana kabari kwance kuma ace yayi Magana!! abun da mamaki). Malam yace kowa ya tafi gida a dawo gobe.
Daren ranar Malam bai rumtsa ba ya kawana nafila da addu'o'i akan wannan lamari.
Washe gari aka dawo Maqabarta tare da Alhj mai rai da yan uwan Alhj mai mutuwa da Lauyoyi da yan sandan kotu, Malam yacewa yan uwan Alhj zansa a tone kabarin Alhj kun yarda? sukace sun yarda Malam yasa aka kira masu gadin Maqabarta yace su tone kabari Alhj nan da nan suka kama aiki, abun mamaki ana bude Kabarin Alhj sai akaga Layuka da Guraye da Daga dasu Karhu dasu Baru kafi uwa-uba... Malam yasa aka kwashe bayan an kwashe yasa aka maida gawar Alhj bayan an rufeta Malam ya matsa kusa da kabarin Alhj ya kira saunansa har aji uku Alhj bai amsa ba, Malam yace, kudin daka mutu ka bari na waye?? Alhj shiru ba amsa Malam ya maimaita tambayar har sau uku shiru ba amsa, sai Malam ya waiwayo ya nuna Alhj mai rai yace ku kamashi Matsafine dukiyar marayu yakeso ya cinye.
To wannan Shari'ace tafi ba Malam mamaki da Al'ajabi a rayuwar Alkalancinsa... fatanmu Allah ka kiyayemu dacin haqqin Marayu kuma yajikan Malam da rahma yasa ya huta,,, kuma Allah yajikan Sauran Al'ummar Musulmi Baki Daya.

0 comments: