Friday, 13 June 2014

Alamommin

┏̲m̶̲̅┓̲┏̲m̶̲̅┓̲┏̲m̶̲̅┓̲ALAMOMIN SO┏̲m̶̲̅┓̲┏̲m̶̲̅┓̲┏̲m̶̲̅┓̲ Akwai alamomin dake fitar da so, masu tarin yawa suke bayyana soyayya ga kadan daga ciki. 1. KUNYA da zarar soyayya ta fara shiga ko da ba a yi furuci ba sai kunya ta shiga tsakani, sai a ga masoyan a junansu suna jin kunyar juna. 2. YAWAN KALLO wannan alamace ta soyayya,misali ta hanyar yawan satar kallo, idan masoyi yana kallon a bin son shi da ya waiga sun hada ido xai kawar da kansa. 3. FADUWAR GABA a lokacin da soyayya ta fara shiga xuciyar saurayi ko budurwa xa ka samu da zarar sun hango juna kowa sai gabansa ya fadi 4. YAWAN AMBATO matukar soyayyar saurayi ta kafu a zuciyar budurwa ko ta budurwa ta shiga ran saurayi xa ka samu yana yawan kawo lbrn wanda yake so din a ko yaushe, kuma duk inda ya ji an fara lbrn wanda yake son xa kaga ya nutsu yana sauraro. 5. TAUSAYI soyayya musamman ta gaskiya tana tare da tausayi. Kuma sau tari zakaga masoyi ko masoyiya suna matukar tausayi ga junansu har hakan na haifar da damuwa ko saurin kuka musamman mata.......
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: