Friday, 13 June 2014

IBB

Hawan IBB shugabancin kasa ke da wuya sai gwamnatinsa ta kwadaitar da mutane, a aikace, za a samu bambancin yanayin siyasa da kare hakkin dan Adam. Nan da nan IBB ya soke dikiri na 4, maras farin jini, kuma ya saki tsararrun da dalilan siyasa suka tilasta wa zaman daffo a gidan maza. Wadannan matakai da ya dauka sun sa ’yan Nijeriya zaton watakila gwamnatinsa ta kulla abin arziki. Ranar 13 ga watan Janairu na shekarar 1986 IBB ya kaddamar da wani muhimmin Kwamitin Nazarin Harkokin Siyasa, wanda zai zagaya kasa domin ya ji ra’ayoyin mutane game da matsalolin da suka yi wa dimokuradiyya tarnaki da kuma shawarwarin hanyoyin da za a bi don cin nasarar magance su. Kwamitin ya kunshi wasu gogaggun masana su 17 a karkashin shugabancin Mista Sylvanus J Cookey. A jawabinsa na kaddamarwa IBB ya ce: “Matsalar tattalin arzikin da kasarmu ke fuskanta sakamako ne na gurbataccen tsarin siyasa da yanayin shugabanci. Ya wajaba mu dukufa wajen samar da ingantaccen tsarin siyasa wanda zai bai wa kowa damar taka rawar da ta dace a harkokin tafiyar da rayuwarsa. Ta haka za mu ci moriyar yawan jama’a da sauran ni’imomin da Allah Ya azurta mu da su, a yunkurin gina dunkulalliyar kasa mai dogaro gami da alfahari da kanta.” Kwamitin ya saurari jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu. Bugu da kari, ya karbi rubutattun makaloli har dubu ashirin da bakwai (27,000) wadanda suka kunshi bayanan da suka shafi: addini da kabilanci da akidu. Kundin Rahoton da kwamitin ya gabatar ga gwamnati ya tattauna dimbin al’amuran da suka shafi harkokin siyasa da jagoranci. Misali, rahoton ya yi wurgi da ra’ayoyin da suka nemi a yi gwamnati ta hadin gambizar soja da farar hula, ko barbarar yanyawar da za ta kunshi soja da ’yan siyasa da sarakunan gargajiya.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: