Labari
An yi wani lokaci da wadansu matasa biyu; Bakano da Bazazzage suke fada, hakan ya sanya mutane suka taru, domin raba fadan. Bayan an raba su sai Bakanon ya kama gabansa, yana fadin “Wallahi sai na yi maganinsa.” To dama Bazazzage yana fama da ciwon ciki, inda a daren ranar ciwon ya sake taso masa har rai ya yi halinsa. Ko da gari ya waye mutane suka ji labarin ya mutu, sai suka fara zargin Bakanon saboda kalaman da ya yi cewa sai ya yi maganin Bazazzagen. Ba tare da bata lokaci ba ’yan sanda suka je suka tasa keyarsa bisa zargin kisan kai. Bakano ya yi magiyar duniyar nan kan ba shi ya kashe Bazazzage ba amma duk a banza. A karshe aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai
Tags:
Musha Dariya

0 comments: