giwa
An yi wata giwa a wani kauye, wadda ba ta tsokanar mutanen garin. Kullum idan ta fito daga gidanta za ta je kogi wanka, sai ta bi ta gaban shagon wani tela. Telan yakan kira ta ya ba ta abinci. Hakan ya sa suka shaku sosai suka zama abokai. Tsabagen yadda ta saba da telan idan ta zo wucewa, sai ta sanya bakinta a shagonsa, shi kuma sai ya ba ta abinci. Rannan tela ya yi fada da masu kawo masa dinki. A takaice dai yana cikin bacin rai, sai giwa ta zo wucewa ta sanya bakinta a shagon tana tsammanin ta ji abinci a bakinta. Sai ta ji ya soka mata allura. Sai ta janye cikin sauri, sannan ta tafi abinta. Daga nan ta wuce zuwa kogi, tana cikin wanka sai lakar cikin ruwan ta toshe mata hanci. Da ta zo komawa gida, sai ta tsaya a gaban tela a kan kayan dinkunnan da aka ba shi ta feso masa wannan tabon, ya bata masa kayansa.
Tags:
Musha Dariya

0 comments: