Monday, 2 June 2014

allah mai iko

BABA ANA GANINKA!!!
Wani Mahaifi Ne Ya Qira 'Dansa Ya
Ce:-
"Zo Ka Rakani Unguwa"
Sai Suka Tafi Suna Cikin Tafiya
Yaro Ya Gaji
Sai Ya Ce:"Baba! Ina Zamu Ne???"
Sai Baban Ya Ce:"Mun Kusa"
Can Sai Suka Isa Wajen Wata
Katuwar
Bishiyar Mangwaro Sai Uban Ya
Ce:-
"Tsaya Nan Zan Hau Amma Fa Idan
Kaga
Wani Ya Taho Kayi Gaggawar Fada
Min Sai In
Sauko Kar Su Kama Ni Ka Ji???"
Yaro Ya Ce:"To Baba!"
Uban Ya Tattare Kayansa Ya Hau
Bishiya Ya
Mika Hannu Kenan Zai Tsinki
Mangwaro Na
Farko Kenan Sai 'Dan Ya Ce:-
"Baba Ga Wani Nan Yana Kallon Mu
Maza Ka
Sauko"
Mahaifi Cikin Firgici Yayi Ta Waige-
Waige
Bai Ga Kowa Ba Sai Ya Ce Da
Yaron:-
"Kai Baka Rabuwa Da Shiririta Kace
Wani
Yana Kallon Mu Ina Yake Banga
Kowa Ba???"
Sai Yaro Ya Ce:"Baba! ALLAH Ne
Yake Kallon
Mu"
Sai Jikin Mahaifin Yayi Sanyi Ya
Gane Cewa
Abinda Yayi Shirin Yi Ba Dai Dai
Bane Ya
Kuma Gode ALLAH Da Yasa 'Dan
Yana Rike
Abinda Ake Dasa Masa Na Tsoron
ALLAH.
ALLAH YASA MU FI QARFIN
ZUCIYOYINMU,
YA BAMU WADATAR ZUCI, YASA MU
GAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEE
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: