SHIN ALLAH ZAI GAFARTA MIN LAIFINA
KUWA???
Wannan labarin wata 'yar uwa ce da ta
samu kanta ciki rudun zamani, kuma tayi
nadama take nemin Allah ya taimake ta ta
bar mummunan laifin da take aikatawa. Ga
yadda labarin na ta yake dalla - dalla: Zan so ku boye sunana sannan ku bani
shawara da taya ni da addu'a akan
labarina, sannan don Allah kar ku zage ni
domin jarrabawa Allah ya nufe ni da
fadawa ciki, kuma babu wanda yafi karfin
Allah ya jarrabe shi. Da farko dai ni cikakkiyar Bahaushıya ce,
mahaifina ya rasu tun ina da aji 5 a
Primary sai na koma hannun yayata
wacce nake zaune a wajenta, bayan na
gama Primary sai aka kai ni makarantar
kwana ta mata (boarding school) a can ne na hadu da gurbatattun 'yan mata wanda
suka lalata rayuwata da abinda har yau
idan na tuna ina kuka da hawaye. Wato
lokacin da aka kai ni ina JSS 1 a dakinmu
akwai yara 'yan mata mu 12 wanda 8
daga cikinsu duk masu dabi'ar neman 'yan uwansu mata ne, wato 'yan LESBIANS, tun
suna yi abun baya bamu sha'awa har
shaidan ya rinjayar damu mu ma muka
fada cikin aikata wannan mummunar
dabi'a. Na yi sanadiyyar shigar da 'yan mata
sama da 20 cikin wannan mummunar
dabi'a. Wallahi wallahi ina mai rantsuwa
har ga Allah kwata kwata bana sha'awar
da namiji ko miskala zarratın amma yanzu
da mace zata gitta se naji sha'awarta ta kama ni. Na yi na yi na daina
wannan hali nawa na kasa sannan duk ran
da banyi masturbating din kaina ba bana
iya yin barci. a gaskiya ina cikin nadamar
rayuwata kuma ina tunanin anya Allah zai
yafemin wannan babban kuskuren kuwa? Zan son nayi amfani da wannan damar
don na janyo hankalin iyaye maza da mata
da su san su wanene kawayen yaransu
dan yanzu haka maganar da na ke yi
akwai kungiyoyin 'yan madigo da na sani
dayawa wanda har da matan manyan mutane a ciki, kuma wallahi wannan dabi'a
yanzu ta watsu cikin hausawa sosai fiye
da yanda kuke tunani dan ana rudar yara
da kudi, kwayoyi, sannan a dandana musu
dadin sex ta hanyar da ba za'a dauki ciki
ba sannan a nuna mata yadda za ta iya biyawa kanta bukata. A karshe ina rokon addu'ar don girman
Allah da ku taya ni addu'ar Allah ya gafarta
min laifin dana aikata, Ya dawo dani kan
hanya madaidaiciya. Hhhhhmmm!!! Wannan ita ce babbar
magana, sai dai 'yar ki sanya a cikin ranki
cewa babu wani laifi da ya girmi Allah yayi
wa bawa gafara inda ba yayi shirka ba. Sai dai bari mu ji irin shawarar da sauran
'yan uwa za su baki ko za ki samu wadda
zaki dauki kiyi amfani da ita
ALLAH yasamu dace
Tags:
fadakarwa

Abdul
ReplyDelete