DAMA TA SAMU FA
(((YAU NE FA, TUN DAGA FADUWAR RANA))) Hakika Uwar Muminai Aisha(radhiyallahu anha) tace: Manzon Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) ya tsaya daga dare yana sallah,sai ya tsawaita sujada har nayi zaton ko an karbi ran Shi ne, da naga haka sai na tashi na je na girgiza babban yatsan Shi, saiko ya motsa sai na koma. Lokacin da ya daukako kan Shi daga sujada kuma ya gama sallar Shi, sai yace: Ya Aisha ko ya Humaira! kin yi zaton Annabi ya kyale ki? Sai nace: A'a wallahi ya Manzon Allah, saidai nayi zaton an zare ranka saboda doguwar sujada da kayi. Sai yace: kin san ko wane dare ne wannan? Sai nace Allah da Manzon Shi suka sani. Sai yace: Wannan dare nisf sha'aban ne, hakika rahamar Allah tana sauka a wannan dare na nisf sha'aban ga bayi, ya gafartawa mai masu neman gafara, kuma yayi jin kai ga masu neman jin kai. Amma yana kyale masu gaba yadda suke. (Imam Albaihaqy) Ya Allah ka gafarta mana, ya Allah kai mana rahama, ya Allah ka hana mu kullacin wani daga cikin bayin ka. Ya Allah ka yarda da mu
Tags:
Addini

0 comments: