munfurci
MENENE TUSHEN MUNAFURCI? : 1. Da farko dai Munafurci wata irin cuta ce acikin zuciya, wacce idan ta kama zuciyar, tana cinye imani ne har sai ya zama babu saura. Daga nan sai Mutum ya zama cikakken Munafuki wato WANDA YAKE BAYYANA IMANI AKQN HARSHENSA, AMMA ZUCIYARSA TANA CIKE DA KAFURCI. Munafukan Farko wadanda suka zauna zamani guda tare da Manzon Allah (saww) sun kasance SUNA SALLAH, SUNA AZUMI, KUMA SUNA RAKA MANZON ALLAH (SAWW) WAJEN YAQI AWASU LOKUTAN. Amma duk da haka Allah (swt) yace "SU FASIQAI NE" Awani wajen ma Allah yayi wahayi ga Annabinsa (saww) cewa : "HAR ABADA KAR KA QARA YIN SALLAH ABISA 'DAYANSU IDAN YA MUTU. KUMA KAR KA QARA TSAYAWA KAN QABARINSA. SABODA YADDA LAMARIN YAKE, SU SUN KAFIRCE MA ALLAH DA MANZONSA KUMA SUN MUTU SUNA FASIQANCI". (Suratut Taubah ayah ta 84). SUBHANALLAH!!! Awani wajen kuma Allah ya gaya ma Annabinsa cewa: "DAIDAI NE AGARESU. KO KA NEMA MUSU GAFARA KO KUMA KAR KA NEMA MUSU GAFARA, ALLAH BA ZAI TA'BA YAFE MUSU BA. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRYAR DA MUTANE FASIQAI. (YANA YIN AZABA GARESU). (Suratul Munafiqun ayah ta 6). Lallai munafurci ba Qaramar chuta bace.. Idan ta kama zuciyar Dan Adam, tana da wahalar ganewa, kuma tana da wahalar warkewa. kuma tana jawowa mai yinta azaba ta har Abada. Amma sai dai Munafurci a mahangar hausawa yana da 'dan bambanci da Munafurci a mahangar Musulunci. Amma insha Allahu zamu kawo muku misalai na irin halayen wadancqn Mutanen wadanda Allah ya tsine musu kuma yace ba zai musu gafara ba, idan sun mutu akan halayensu. Ya Allah ka tsare mana zukatanmu daga halayen Munafurci.
Tags:
Addini

0 comments: