Wednesday, 11 June 2014

hattara dai

Wallahi ka so mai sonka ka zauna lafiya!!! A wani kauye a Karamar Hukumar Gamawa da ke Jihar Bauchi, a ka yi wani Mutum da ya ga wata Yarinya, ya ji yana sonta, ya je ya same ta ya kuma sanar da ita, ta ce ita kuma ba ta son sa, ta na da wanda za ta aura, mutuminnan ya matsa da zuwan mata da bukatarsa na ta so shi, yarinya ta ce sam ba ta son shi, to da ya ke mutumin ya na da rufun asirinsa, sai kawai ya biyo mata ta sama, ya je ya samu iyayenta ya masu yayyafi na Kudi, su ka ce masa ya kwantar da hankalinsa kamar ya aure ta ne, su ka yiwa yarinya dole ta Aure shi ba dan ta na son shi ba, bayan sun samu shekaru uku da aurensu, sun haifi 'ya 'ya biyu, wata rana matar ta na zaune a tsakar gida ta na baiwa karamin danta nono, sai mijin ya shigo, bayan sun gaisa sai mijin ya ce mata, oh!!! wance kenan kamar ba ke ce ki ka ce ba kya so na ba, lokacin da na ganki na je gidan kafin aurenmu, sai ita kuma ta ce masa kai a tunaninka yanzun sonka na ke yi? sai kawai mike ta shiga cikin daki inda daya yaro ya ke kwance ya na barci, ta dauko shi ta fito waje, shi kuma tsaya ya na kallon ikon Allah, ta na zuwa sai kawai ta kama kafafun yaro da ya ke a hannunta ta daga shi sama, ta tamfatsa shi a kan jaririn da ya ke kwance a kan tabarma, duk suka mutu ita kuma ta ficce daga gidan, ta barshi a firgice cikin rudani, Ya Allah ka hada mu da masu sonmu ba wadanda mu muke sonsu su ba sa sonmu ba.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: