allah sarki baiwa
Wani kare ne yaje wajen wani malami yace alagafarta malam inaso ne abani wani lakanin da zan dinga amfani dashi wajen kama mage, saboda naga yanzu suna bani wahala kafin na kamasu shine nakeso a taimaka mun, sai malamin yace to ka dan saurara kadan ka jira ni kafin na gama aikin da nakeyi... Kare ya nemi waje ya zauna yana jiran malam, can sai ga kura tashigo wajen malam itama tazo neman taimako, tace malam ina son a taimaka mun da lakanin da zan samu abunda zanci yanzu kwana na ukku (3) banci komai ba yunwa kamar zai kashe ni, karen nan yanajin haka sai ya fara zare ido, sai malamin nan ya amsa mata yace to ba damuwa ki dan saurara, sai malamin ya juya bangaren kare yace kai menene bukatar taka sai kare yace na canza shawara malam abunda nakeso yanzu kawai ka taimakamun da lakanin da zan koma gida na lafiya ba tare da wani abu yasameni ba.
Tags:
Abin Mamaki

0 comments: