YA KAI DAN ADAM!!! MENENE YA RUDEKA
HAR KA MANTA DA BIYAYYAR UBANGIJINKA
NE??
★ Idan jin dadin duniya ne yake rudarka, to
fa gaba daya rayuwar duniyar nan bata kai
tsawon wuni guda na rayuwar lahira ba.
★ Idan kudi ne suke rudarka, to fa ka sani
komai yawan kudinka anan duniya zaka
barsu.. Ba za'a binneka da ko sisi ba.
★ Idan Kyawun Matanka ne yake rudarka, to
fa ka sani da zarar ka mutu, Matanka zasuyi
rige-rigen kwasar ganimar dukiyarka ne..
Sannan daga baya suyi rige-rigen aurar wasu
Mazajen..
Watakil ma acikin gidanka wani angon zai
tare da Matarka!!!!
★ 'YA'YANKA : tunaninsu shine araba
dukiyarka abasu nasu kason, Mai hankali
acikinsu shine wanda zai tuna dakai idan
yayi sallah yayi maka addu'a..
Amma wani ma sai yayi watanni bai tunoka
ba.. balantana yayi maka wata addu'a ta
musamman!!!.
★ GIDANKA : Kana mutuwa, wata sabuwar
rayuwar za'a sake yi acikinsa..
★ MOTICINKA : Ko sun kai 100, idan ka mutu
aciki PICK UP (AKORI-KURA) za'a sanyaka...
ita ce abin hawanka na Qarshe!!.
★ ABOKANKA : Indai alakarku bata ginu
abisa bin Allah da Manzonsa ba, to aranar
lahira sai kun tsine ma juna agaban Allah!!.
★ IYAYENKA DA DANGINKA : Ba zasu
amfaneka da komai ba awajen Allah...kuma
ba zasu taimakeka ba.. kowa ta kansa yake
yi!!.
Gara ma ka tuba kabi Allah da Manzonsa tun
lokaci bai Qure maka ba!
Allah yayi mana kykyawan karshe ameen FROM ALIYU RABI'U SHEHU.
ya kai dan uwa
Tags:
fadakarwa

0 comments: