Saturday, 5 July 2014

brawoa

* BARAWON BABUR * Wani ne matarsa ta haifi jaririn da bai zo da rai ba a asibiti, sai ya samu babban kwalin biskit ya saka gawar jaririn a ciki, ya dora a kan babur. Ya bar babur din a kafe, ya je cikin asibiti domin ya sallami likita. Ko da ya dawo sai ya samu an sace babur da gawar da ke cikin kwalin. Barawon yana tafiya sai ya hadu da ’yan sanda, ya ciro Naira dari ya ba su, ya ce: “Oga ina sauri ne!” Wani dan sanda ya ce: “To ka ba mu biskit din mana muma mu ta6a.” barawo ya bude kwalin da nufin ciro biskit, sai ga gawar jariri kwance. Sai barawo ya ce: “Wallahi oga ni ba barawon yara ba ne, ni barawon babur ne!” barkanku da shan'ruwa SAHIBUL-KALAAM
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: