hmmm
*Hmm mutanen wancan gari akwai hikima* Wani mutum ne mai hikima yana cikin tafiya akan wata hanya da ba mutane dauke da dukiyar matarsa, sai ga wani barawo ya yo kansa rike da wata bindiga, sai ya ce ma sa "bani abin da ke hannunka ko kuma in kashe ka." Sai wannan mutumin mai hikima ya ba shi, barawon har ya juya zai tafi sai mutumin ya ce masa "ina rokon wata alfarma da ka harbi hulata sau daya saboda kada matata ta zarge ni da yi mata karya kan wannan dukiyar. Sai barawo ya harbi hularsa, ya juya zai tafi sai kuma wannan mai hikima ya kara rokar barawo da yayi ta harbin gefen babbar rigarsa, saboda matarsa kada ta ce ya bada dukiya saboda harbi daya, sai barawo yayi ta harbin gefen rigarsa har sai da harsasan bindigar suka kare, sanna ya ce wa mutumin kayi min uzuri saboda harsasan dake cikin bindigata ya kare. Ko da jin haka sai wannan mai hikima yayi wuf! ya rike barawon ya ce dawo min da dukiyata, sai barawo ya mayar masa da dukiyarsa..kuka san mutanen wane garine suke da hikima irin haka??
Tags:
Musha Dariya

0 comments: