Monday, 7 July 2014

computer

Muhimman Ayyukan Babbar Manhajar computer Hanya ta biyu na samuwa ne ta tsarin “Plug and Play” ko “PnP” a gajarce. Wannan shi ne tsarin da ke tabbatar da alaka tsakanin kwamfuta da duk wani abin da aka makala mata na sadarwa – musayar bayanai wajen shigarwa ko karba. Tsarin “PnP” wani ginannen tsari ne da kamfanin Microsoft ya fara gina shi tun a babbar manhajarsa mai suna “Windows 95,” babbar manhajarsa ta farko da ta fara yin fice, kafin nau’in Windows XP ta maye gurbinta. Tun sannan kamfanin Microsoft ke dada inganta wannan tsari, don taimaka wa masu mu’amala da kwamfutar da ke dauke da Babbar manhajar Windows iya mu’amala da bayanan da suke son shigar wa kwamfutar, kai tsaye. Yadda tsarin yake shi ne, da zarar ka soka ma’adanar filash (Flash Drive) a jikin kwamfutarka misali, nan take babbar manhaja za ta tsara (Configure) wannan ma’adana, sannan tana iya budo maka abin da ke dauke cikinta (Autoplay) na bayanai nan take (kana iya hana ta yin hakan a bangaren “Control Panel” don kare ta daga kwayoyin cutar kwamfuta masu shigar da kansu nan take da zarar babbar manhaja ta karbi ma’adanar da aka shigar mata). Wannan tsari na “Plug and Play” na da alaka ne na kai tsaye da babbar titin sadarwa da ke jikin kundun kwamfuta, wato “Computer Bus.” Hanya ta uku da babbar manhajar kwamfuta ke hada alaka a tsakaninta da gangar-jikin kwamfuta shi ne ta rumbun adireshin masarrafai, wato “System Registry” kenan. Wannan cibiya babbar matattara ce dake dauke da bayanin inda kowace manhaja ko masarrafa ke ajiye a kwamfutar. Idan kana son fahimtar wannan rumbu ka dubi bangaren adana bayanan ma’akatan gwamnati ko hukumomi, wato “Registry.” A wannan wuri ne jakar bayanin sirrin (Secret File) na kowane ma’aikaci yake. Da zarar ka loda (Install) wa kwamfutarka sabuwar manhaja ko masarrafa (Application/Software), babbar manhaja za ta taskance adireshin inda wannan manhaja da ka loda take. Ba manhaja kadai ba, hatta na’urar da ka jona wa kwamfutarka, ko da kuwa sau daya ne, nan take babbar manhaja za ta adana suna da lambar wannan na’urar da ka jona wa kwamfutarka. Da zarar ka sake jona mata a karo na biyu, nan take za ta fahimci cewa a baya an taba loda mata shi, ba sai ta sake neman loda ‘yar karamar masarrafar da ke dauke a na’urar ba, wato “Driver.” Wannan runbum adireshin bayanai na dauke ne da adireshin duk wani abu da ke tattare da kwamfuta; masarrafa ce, manhaja ce, ko na’ura ce da ke makale a jikinta ko ake jona mata lookaci-lokaci. Idan kana son ganin wannan rumbun adireshin manhajoji da na’urori, ka je “Start” (idan Widnows 7 ce, ko kasa ta ita), sai ka rubuta “regedit” ka matsa “Enter” nan take za a budo maka. Amma fa ba za ka iya fahimtar komai a ciki ba idan ba kwararre bane kai. Domin lambobi ne da wasu kalmomi da kwararru ne kadai ke iya saninsu, a makare a ciki. Wannan shi ne aiki mai muhimmanci na farko da babbar manhajar kwamfuta ke yi; wato hada laka tsakaninta ko tsakaninka da gangar-jikin kwamfutar baki daya. Domin wannan shi ne abin da ke tabbatar da matsayinta da a baya nace: “Babbar manhajar kwamfuta ce ke tafiyar da kwamfutar baki daya.” Ka ga kuwa idan ya zama ba ta iya hada alaka tsakaninka ko tsakaninta da gangar-jikin kwamfutar, ba kanta kenan, wai Dansanda ya rasa idanu.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: