hmm
Kyal kyal kyal Waı da gaske ne ba'ayıwa mata gwanınta? wani mutum ne yana zaune da matarsa kimanin shekaru ashirin wataran bayan yaje masallaci anyi sallar jam'i sai liman yafara yiwa mutane nasiha kamar haka: "Jama'a kudinga kyautatawa matayen ku misali" Idan matarka ta kawo ma abinci sai kace mata nagode kuma abincin nan yayi dadi sosai, sai taji dadi sosai sabida mata nason hakan. Bayan liman yagama nasihar sa sai mutumin nan yakoma gida, can sai matarsa takawo masa abinci tazuba masa sai ya sa hannu ya dan taba sai yace kai abincin nan yayi dadi, Allah ya saka da alkhairi yana kuma murmushi. Da matar taji haka sai ta bata rai ta dauki ludayin miya ta kwada masa a kaı {kwal} Sai kuma tasa kuka sai hankalin sa yatashi yace mata me yafaru haka? Sai tace masa yau shekaranmu wajen ashirin amma baka taba cemin abincina yayi dadi ba sai da makwabta suka kawo wannan abincin zaka ce min yayi dadi har da addu'a In kaıne ya zakayı
Tags:
Musha Dariya

0 comments: