Friday, 3 October 2014

ILLOLIN DA MADIGO KE HAIFARWA GA MASU YI **Lesbianism**

Madigo shi ne mace ta
biya
bukatarta da mace, ta
hanyar
rungumar juna da hada
gaba.
Madigo haramun ne a
addinin
Musulunci. Malamai sun
sanya
shi daga cikin manya-
manyan
zunubai.
1- Sai dai shari’a ba ta
bayyana wani hukunci
zaunanne da za a yi wa
masu
madigo ba, alkali ne zai
duba
me ya dace ya yi musu
na
hukunci, bulala ko dauri
ko
kora ko tozartawa, ko
kuma a
hada musu duka.
2-Wasu malaman suna
ganin za ayi musu
hukuncine dai-dai da na
yan Luwadu. Duk dai
hukuncin da alkali ya
yanke na razanarwa da
tsoratarwa yayi.(Duba
Al-
mausu’atul Fikihiyyatul
Kuwaitiyya da Almugni
na
Ibnu kudama).
*Illolin Madigo*
kamar sauran abubuwan
da suka gabata ne wajen
haifar da
cututtuka da bala’i da
musiba
ga mai yinsa da kuma
kasa
baki daya. Ga kadan
daga
cikinsu:
1* Madigo tana canzawa
mace halittarta
daga dabi’ar da Allah Ya
halicceta da ita, ta koma
tana sha'awar mace ’yar
uwarta.
2* Cikin Madigo
akwai rashin kunya da
fitsara,
alhali Manzon Allah
(S.A.W)
yana cewa : “Kunya
alheri
ce
gaba dayanta”. A wata
ruwaya : “Kunya ba ta
kawo
komai sai alheri”.
(Bukhari
ne
ya rawaito).
3* Madigo yakan
haifar da cutakan
zamani.
A
wani bincike da aka
gabatar
ya tabbatar da za a iya
daukar
cutar KANZAMAU ta
hanyar
madigo, idan aka yi da
wadda
take dauke da ita, kamar
yadda za a iya samun
ciki
ta
hanyar madigo, idan
mace
ta
yi da wadda ba ta dade
da
saduwa da da namiji ba.
4* Haka nan likitoci sun
tabbatar da madigo
yana
iya jawo rashin haihuwa.
5* Ana iya rasa
budurci ta hanyar
madigo,
wanda hakan ba
karamin
tozarta ba ne ga
budurwa
ta
rasa budurcinta kafin ta
yi
aure.
6* Mai madigo takan
rayu cikin kuncin zuciya
da
kunarta, saboda Allah zai
debe mata natsuwa a
tare
da
ita, Ya maye gurbinta da
kunci
da damuwa.
7* Madigo yakan
hana ’ya mace zaman
aure,
domin duk wadda ta
saba
da
shi, to zai yi wahala kafin
ta
rabu da shi, wanda
wannan
zai sa ta kasa wadatuwa
da
mijinta, sai ta rika fita
tana
yi,
har idan Allah Ya tona
asirinta,
mijinta ya sake ta, saki
na
wulakanci, ko kuma ta
nemi
saki da kanta ta je ta ci
gaba
da madigonta.
8* Duk Mai madigo idan
bata tuba ba, bata
Gamawa da duniya
lafiya,
ko
dai tozarta a duniya, ko
kuma
haduwa da mummunar
cuta
da bala’in da ba a
warkewa,
sai dai kabari!
9* Madigo
dabbanci ne, saboda ko
Dabbobi mata ba sa yin
madigo.
10* Cikin madigo
akwai cin amanar Allah
Mahalicci, saboda an
aikata
abin da Ya hana, haka
kuma
akwai cin amanar iyaye
ko
miji.
11* Haduwa da azabar
Allah a lahira, idan ba a
tuba
ba
12* Madigo gaba
dayansa
kazantane!!!
YA ALLAH KA KARE YAN
UWANMU MUSULMAI
DAGA WANNAN BALA'I,
YA ALLAH KA KARE
MUSULUNCI DA
MUSULMAI.........AMEEN
Previous Post
Next Post

About Author

1 comment:

  1. khadeejah modibbo13 June 2016 at 15:13

    Ubangiji y shirye masu ae katawa

    ReplyDelete