Friday, 14 November 2014

babu rabin xance

BABU BATU!



Wani Basakkwace ne ya je Kano ci- rani, sai ya sayi babur domin yin acaba. Wata rana sai ya biyo ta titin da ba a bi, sai sojoji suka tare shi suka kwace mabudin babur din suka kai wa babbansu.



Ashe Basakkwace na da wani mabudin a aljihunsa, sai da ya faki idanun sojojin, sai ya dauko ya sa a babur din, kafin ya tashi babur sai ya kwala wa babban cikinsu kira ya ce: “Oga, mabudin da ka sa aka kwace a guna, na ba ka kaje ka kai wa gyatumarka.” Sai ya buga babur don ya gudu har sau tara, babur ya ki tashi. Sai ya ce “Assha! Babu batu yau.” Sai ya kafe babur ya fara tsallen kwado tun kafin Oga ya karaso wurinsa.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: