* Sayyiduna Abubakrin Shine kadai Sahabin da Iyayensa Ma Sahabbai ne, 'ya'yansa ma duk Sahabbai ne, Matansa ma haka.
* Sayyiduna Abubakrin Sau uku yana kyautar da dukkan dukiyarsa don ci gaban Musulunci.
* Sayyiduna Abubakrin watarana wani Bawansa ya bashi wata Tuffah yaciaa, har ya fara ci sai ya tsaya ya tambayeshi "Shin a ina ka samu wannan Tuffar?"
Sai yace : "Ai wani mutum ne ya bani ita, kuma dama Tun lokacin Jahiliyyah ina yi masa BOKANCI ne. Shi yasa ya bani"
Jin wannan zance keda wuya sai Sayyiduna Abubakr ya sanya hannunsa cikin bakinsa ya Kakalo Amai, ya amayar da dukkan abinda yaci awannan ranar.
* Sayyiduna Abubakrin ya taba sanya Qafarsa ya toshe Kofar wani ramin Maciji don kare lafiyar Manzon Allah (saww). Shi kuma Macijin yana so ya fito ya gaisar Da Manzon Allah (saww) don haka Macijin yayi ta Cizonsa amma bai dauke Kafar ba har sai da Manzon Allah (saww) ya farka daga barci yayi masa addu'a.
* Sayyiduna Abubakar bai taba bautar Gumaka ba, bai taba shan giya ba, bai taba chacha ba.
* Lokacin da zai rasu ya bar Matarsa da ciki, Kuma ya gaya mata cewa Mace zata haifa. Kuma Macen ta haifa.
Ya Allah ka Qara yardarka gareshi da dukkan Sahabban Manzon Allah (saww). Mu kuma ka Qara mana Soyayyarsu da Girmamawa, da kuma tafiya bisa tafarkinsu har karshen rayuwarmu.
ABUBUWAN MAMAKI GAME DA SAYYIDUNA ABUBAKAR
Tags:
Addini

0 comments: