Saturday, 15 November 2014

YA MUTU SABODA TSORON JAHANNAMA!!

Ibnul Mubarak yace Muhammad Ibnul Mutarrif ya bamu labari cewa:


Azamanin Manzon Allah (saww) Akwai wani saurayi Mai mutakar Tsoron Allah daga cikin Ansar (Mutanen Madeenah) wanda duk lokacin da ya tuno da Wutar lahira da kuma azabar cikinta, sai ya zauna yayita Zabga kuka, har saboda tsananin Tsoro da kuma firgita sai ya zauna agidansa ba ya iya fitowa cikin Jama'a.


Da aka sanar da Manzon Allah (saww) halin da wannan saurayin yake ciki, sai ya taho zuwa gidan wannan Saurayin tare da Manyan Sahabbansa (rta).


Yayin da Manzon Allah (saww) ya Shiga gidan wannan saurayin, yana ganinsa sai ya tashi ya rungumeshi. Kuma nan take ya fadi ya mutu.


Sai Manzon Allah (saww) yace ma Sahabbansa "Ku Gyara Dan Uwanku (kuyi masa jana'izar) Domin hakika Tsoron Wutar lahira ne ya Yanke masa Zuciyarsa".


Hakama Salmanul Farisiy lokacin da aka saukar da ayar nan ta 43 acikin Suratul Hijri, sai da yayi Kwana Uku bai fito wajen Mutane ba. Yana zaune agida yana Kuka!!!


Ayar tana cewa: "Kuma Hakika Jahannama ce Makomarsu baki dayansu".


Wannan ne ya bashi tsoro domin kuwa ayar tana magana ne akan 'Yan Adam wadanda suka yarda da shaitan har yayi musu wasa da zuciyarsu.


Salmanul Farisy yana tsoron kar ya zama daga cikinsu. Allahu Akbar!!


Wadannan fa Sahabbai kenan!
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: