WAISHIN WA ZAMU SO IDAN BAMU SO ANNABI S.A.W BA ? Amsar itace BABU
Manzon Allah s.a.w shiya sanar damu Allah alokacin da bamusan kanmuba
Shi yazo mana da sallah, zakka, azumi da sauran Ibadu
Shine wanda yayi mana gatan da ko mahaifanmu basuyi manaba, ya fitar damu daga duhun rashin sani izuwa hasken musulunci
Shine wanda Allah ya daukakamu saboda shi
Shine wanda yake nema mana sauki da rahma da rangwame awajen Allah s.w.t
Shine wanda da yaje ganawa da Allah, Allah yace me ka keso baice komaiba sai yace ceton Alummata Shine wanda da yazo wafati s.a.w babu abinda yake fada sai ALUMMARSA yana cewa ya Allah ka kula da Alummata
To yakai dan'uwa yanzu kana da masoyin dayakai wannan, amsar " Babu "
Ya Allah ka kashemu akan soyayyar shugaba ja gaba s,a,w
WAISHIN WA ZAMU SO IDAN BAMU SO ANNABI S.A.W BA ? Amsar itace BABU
Tags:
Addini

0 comments: