Sayyiduna Salmanul Farisy ya rungume Manzon Allah (saww) yana kuka yana sumbartar Khatimin Annabta wanda ke jikin Manzon Allah (saww).
Dukkan mutanen da suke wajen, abun ya basu mamaki sosai. Har sai da Manzon Allah (saww) ya umurci Salmanul Farisy (ra) ya gaya musu labarin rayuwarsa tun daga Farko har zuwa haduwarsu da Manzon Allah (saww).
Daga nan sai Manzon Allah (saww) yace ma Salmanu "Kace ma Ubangidanka ya rubuta maka adadin abinda zaka biyashi domin ya baka 'Yancinka".
Wannan Bayahuden (Ubangidan Salmanul Farisiy) sai yace Ba zai sallameshi ba, har sai ya shuka masa bishiyoyin dabino guda dari (100) kuma har sai lokacin da Bishiyoyin suka fara 'ya'ya. Sannan kuma ya fadi wani adadin Zinare mai yawa, yace sai Salmanu Ya bashi.
Don haka sai Manzon Allah (saww) ya umurci Sahabbai su taimakawa Salmanul Farisiy domin ya samu abinda zai bayar.
Kowa ya kawo nasa taimakon. amma daga Qarshe Manzon Allah ne (saww) ya dauko wani dunkulen Zinare (Gold) ya bashi yace masa "Kaje a auna da nauyin wannan. Insha Allahu wannan zai biya maka abinda ke kanka".
Salmanul Farisy yaga abin kamar Qankani, sai Manzon Allah (saww) yace masa "YA SALMANU, DA ACE ZA'A AUNA NAUYIN WANNAN ZUNAREN, DA KUMA NAUYIN DUTSEN UHUDU, TO SAI WANNAN ZINAREN YA RINJAYA"
Don haka Salmanul Farisy yaje aka dora wannan Dunkuken zinare akan Sikeli sai gashi nauyinsa yakai yadda suke Bukata.
Manzon Allah (saww) yasa aka nemo Qananan bishiyoyin dabino wadanda za'a shuka, Shi da kansa yazo ya rika shukawa da hannayensa masu albarka.
Dukkan dabinan nan guda dari sai da suka fidda 'Ya'ya awannan shekarar. in banda Guda biyu wadanda Sayyiduna Umar bn Khattab ya shuka. Su dinma da Manzon Allah (saww) yaga haka sai ya ciresu ya sake dasawa. kuma awannan shekarar suma suka fara 'Ya'ya.
Salmanul Farisiy ya samu 'Yancinsa daga hannun Yahudawa.
GWARZON MUSULUNCI, SALMANUL FARISY (KASHI NA 3).
Tags:
Addini

0 comments: