Wani ma'aikacin filin jirgin sama ne, aikinsa shine
share-share ciki da wajen jirgi. Kwatsam ran nan
yana cikin shara sai ya tsinci wani dan littafi, a
rubuce a bangon littafin an rubuta "KOYON JIRGIN
SAMA A SAUKAKE"
Ya yi murna kwarai ya wuce kai tsaye gun da direba
ke zama, sai ya ga wasu madannai masu kala-kala
birjik a wuri guda. Sai ya bude dan littafin nan, shafin
farko ya ga an rubuta: 'Idan kana son kunna jirgi
danna madanni fari' sai ya danna fari, injinin jirgi ya
soma aiki.
Ya bude shafi na biyu, ya ga an rubuta: 'Idan ka na
son kulle kofofin jirgi danna kore' sai ya danna koren
maballi, kofofi suka kulle. Ya bude shafi na gaba ya
ga an rubuta: 'Idan ka na son jirgi ya fara gudu a
kasa danna shudi', ya danna.
Haka ya yi ta yi har lokacin da ya tsinci kansa a
sararin samaniya ya na keta hazo. Lokacin da ya
gama shawagi a sararin Subuhana, sai ya yi niyyar
saukar da jirgin kasa, sai ya bude shafin karshe na
littafin, sai yaga an rubuta: 'YADDA ZA'A SAUKAR DA
JIRGI SAI A LITTAFI NA BIYU'
Idan kai ne ya za ka yi?
KOYON JIRGIN SAMA A SAUKAKE
Tags:
Musha Dariya

0 comments: