Wednesday, 5 November 2014

Azamanin Ibrahimu bn Ad'hama akwai wani mutum mai Arziki. Ga kudi ga dukiya mai yawa duk Allah ya bashi.

Watarana ya tattara kudinsa gaba daya ya ajiye arumfarsa ta kasuwa, sai akayi gobara akasuwar har shagonsa ya kone tare da dukkan dukiyarsa da kudinsa.


Saboda tsabar tashin hankali da kuma bakin ciki, sai mutumin nan ya haukace, har yana tafiya yana sambatu.. yana wasu zantuka wadanda ba'a fahimta.


Rannan sai suka hadu da IBRAHIMU BN AD'HAMA (rah) sai yace masa:


"YA KAI BAWAN ALLAH!! WANNAN DUKIYAR FA TA ALLAH CE.. GANIN DAMARSA NE TASA HAR YA JIYAR DA KAI DADI TA HANYAR WANNAN DUKIYAR.


YANZU KUMA TUNDA YAGA DAMA YA KARBI ABUNSA, BAI KAMATA KAYI BAKIN CIKI BA, BAI KAMATA KA FIRGITA BA.


DOMIN KUWA, HAKURI ABISA AFKUWAR MUSIBA YANA DAGA CIKIN CIKAKKIYAR GODIYA ABISA NI'IMOMIN ALLAH DA KUMA LAFIYAR DA YA BAKA...


Mutumin nan yana jin haka sai ya wartsake. ya dawo hayyacinsa..


ALLAHU AKBAR!!
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: