Wani saurayi ne a makaranta, ya shiga dakin
karatu
(library) da shigarsa sai ya hango wata
kyakkyawar budurwa a gefe zaune ita kadai,
kun san halin samari da son hulda da 'yan
mata masu kyau, gogan naku sai ya isa inda
take yai mata sallama, sai yace mata na ganki
ke kadai zaune, shine naga bai dace
kyakkyawar mace kamarki ta zauna cikin
kadaici ba, shine nace bari na zo na tayaki
hira, kawai sai budurwar cikin daga murya
tace "KA GA MALAM NI BA 'YAR ISKA BA CE DA
ZAKA CE IN BIKA DAKINKA IN KWANA KAJE CAN
KA NEMI 'YAR ISKA IRINKA" gaba daya hankalin
mutanen dake wurin ya dawo kansu,
saurayin yaji kamar kasa ta tsage ya shige ciki
don kunya,
bayan mintuna kadan sai budurwar tazo inda
yake tayi kasa da murya tace masa ina
karatun psychology ne na iya karantar abinda
ke ran mutum, ko ban tambayeka ba na san
kaji kunya da abinda nayi ma, saurayin shima
sai ya buda bakinsa da karfi yace "KWANA
DAYA A DUBU HAMSIN (50000) GASKIYA SUNYI
YAWA, HALA AN FADA MAKI SATA NAKE YI?"
gaba daya hankalin mutanen wurin ya sake
dawowa kansu, wasu suka dinga yi mata
dariya suna cewa ashe duk kanwar ja ce,
saurayin ya kalleta shima yayi kasa da murya
yace mata ina karatun law ne na san hanyoyin
kama mutum idan yayi min laifi.
SHIN DA SHI DA ITA WA YAFI KWARAR WANI,
WA KUMA AKA FI MUZANTAWA??
yar psychology da dan law
Tags:
Musha Dariya

0 comments: