MUTUWA TA MANTANI INJI TSOHO DAN SHEKARA 179
Wani tsoho dan qasar India mai suna Mahashta
Murasi wanda aka haifeshi tun shekarar 1835 ya
koka dangane da rashin daukarsa da mutuwa bata
yi ba bayan ya kwashe shekara dari da sabain da
tara a duniya. tsohon yace "Mutuwa ta mantani
tunda ta dauke dukkan 'ya'yana da jikokina da wasu tattaba kunnena amma ni gashi har yanzu" Tsohon wanda ya fito daga garin Bangalore dake
kudancin Qasar an tabbatar da cewa shine wanda
yafi kowani dan Adam a zamanin nan dadewa a
duniya kuma ya samu shaidar haka daga hukumar
kundin tattara abubuwan mamakin duniya wato
GUINESS WORLD RECORDS. Dattijo Murasi ya qara da cewa shi ya saqadar da
mutuwa domin bai san lokacin da zata zo ba kuma.
A yanzu dai yana da shekara 122 da yin ritaya daga
aiki kuma yana cigaba da rayuwa daidai da ta masu
shekarunsa.

Shi malam tsoho banda abinsa,ai ita mutuwa ba ta dagawa kowa kafa,in dai lokacinsa yayi bai isa ta kara masa ko da second daya ba.
ReplyDelete@Sabi'u Abdullahi Natade,
ReplyDeleteGaskiyanka aboki