Bayan Salamanul Farisiy (ra) ya musulunta, sai aka tambayeshi "Shin da wanne suna zamu nasabta ka?".
Sun tambayeshi hakane saboda abisa al'adar larabawa, ba'a kiran sunan mutum kai tsaye. Sai dai ahada da sunan Mahaifinsa, Kamar ace IBNU UMAR, IBNU ABBAS, etc.
Ko kuma ahada da sunan Dansa ko Dan dan uwansa. Kamar ace "Abud Darda'i, Abu Talha, Abu Hafsin, etc.
Amma shi Salmanul Farisi da ya tashi mayar da jawabi sai yace : "Sunana SALMANU IBNUL ISLAM! ".
Allahu Akbar!!
Nan take sai Manyan Sahabbai irin su Sayyiduna Umar suka fashe da kuka!! Suna cewa "Mu mun kasance muna alfahari da sunan iyayenmu, yau ga wani ya shiga musulunci ayau din nan amma har yafi mu. Domin shi
yana Nasabta kansa ne zuwa ga Musulunci".
Shi kuwa Musulunci shine babban abin alfahari domin yafi iyaye da dukkan dangi da kowa ma baki daya.
Allahu Akbar!! Kunji Salmanul Farisy, Amintaccen Allah da Manzonsa (saww).
SALMANU IBNUL ISLAAM
Tags:
Addini

0 comments: