Sunday, 2 November 2014

wata rana manzo (SAW)

Watarana Annabi (s a w) yanatafiya yazo wucewa agaban wata makabarta tareda sahabbansa, sai akaga yatsaya cak akan wasu kaburra guda biyu.


Sai ya tsinko ganyen dabino yarabashi a gida biyu, sai yasoka akan wadannan kaburra guda biyu.


Sai yace "wadannan kaburra anayimasu azabane"
wannan ganyen dabino zai dinga yimusu tasbihi yana nema musu gafara awurin ubangiji kafin yabushe za a saukaka musu azaba.


sai sahabbai suka tambayesi "ya RASULLAHI laifin me sukayi akeyimusu azaba"?


Annabi (s a w) yace "daya munafikine yana daukar zancen wannan yakaiwa wancan.


Dayan kabarin kuma baya tsarki ajikinsa idan yayi fitsari bayayin tsarki kokuma yana fitsari akan dutse fitsarin yana dawo masa ajiki.


Allah kabamu ikon gyara kuskurenmu kuma kadoramu akan tafarki madai daici ameen.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: