Assalam malam dafatan kana lafiya, Malam tambayana ita ce SHIN ya halasta mutum ya auri mace alhalin mijinta yai mata saki uku don ya daidaitasu, sabida ganin halin da suke ciki amma ba tare da yayi hakan da shawaran dayansu ba, sai dai saboda ganin irin matsalar da wadannan ma'auratan suke ciki.. kamar yawan yara dan kadda 'ya'yan su tagayyara, ko kuma su rasa samun ingantacciyar tarbiyya..
AMSA
****
Wa alaikumus salam.
Hakika wannan irin auren bai halatta ba. Kuma yin hakan yana daga cikin manyan laifuka a Musulunci.
Wani ya tambayi Sayyiduna Abdullahi bn Umar bn Khattab (ra) irin wannan tambayar da kayi min. Sai yace "Wallahi bata halasta gareshi ba. Mu mun kasance (Azamanin Manzon Allah -saww- muna Qirga wannan amatsayin Karuwanci ne".
Sayyiduna Uqbatu bn Aamir (ra) yace : Manzon Allah (saww) yace : "SHIN IN BAKU LABARI GAME DA BUNSURUN ARO? " sai Sahabbai suka ce "Kwarai ya Rasulallahi".
Sai yace "MAI AUREN MACE DOMIN HALASTATA GA WANI (SHINE BUNSURUN ARO). ALLAH YA TSINE MA MAI AURAR MACE DOMIN HALASTATA GA MIJINTA. DA KUMA SHI WANDA AKE NEMAN HALASTATA DOMINSA DIN".
(ibnu Maajah ne ya ruwaitoshi da Isnadi Sahihi).
Abdullahi bn Shuraik Al-aamiry (ra) yace Naji anyi ma Ibnu Umara irin wannan tambayar sai yace : DUKKANINSU MAZINATA NE KODA SUNYI ZAMAN SHRKARA ASHIRIN".
daga cikin Manyan Sahabbai da tabi'ai da Tabi'ut tabi'ina wadanda suka bayar da fatawar rashin halaccin irin wannan auren, akwai:
Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib.
Sayyiduna Umar bn Khattab.
Sayyiduna Abdullah bn Umar.
Sayyiduna Abdullah bn Abbas.
Sa'id bn Almusayyib.
Hasanul Basary.
Imam Malik bn Anas.
Imam Sufyan Ath-Thawree.
Imam Shafi'iy.
Imam Abu Hanifa.
Imam Ahmad bn Hanbal.
Imam Isma'il bn Sa'eed.
Ibrahimun Nakha'iy.
Dukkansu Allah shi Qara yarda dasu baki daya.
Daga
karshe ina jan hankalinka, kar ka bari shaitan ya biyo maka ta hanyar sha'awa don yayi maka wasa da hankalinka ya jefaka aramin hallaka.
Wallahu a'alam.
AUREN MACE DOMIN MIJINTA YA SAMU DAMAR MAYAR DA ITA.
Tags:
fadakarwa

0 comments: