Ka'ida ta Allah SAW bai taba sanya Haramun ta
magance
haramun ba.
Ka tambayi duk wani Mashayin giya
akan ya
taba shan giya ya daina jin kishi. Ko kuma ta taba
kawo masa
kwanciyar hankali da natsuwa?? Tambayi duk
wani
barawo
ko dan fashi, shin kudin da ya sata ya taba
magance
masa
baqin ciki ko larura?? Tamabayi mai cewa yana
shan kayan
mayene dan ya samu tinani ko kuma nishadi,
shin
bayan ya
bugu ya dawo daidai damuwar na nan kokuwa??
Tambayi
duk wata mace mai shan syrup, shin ta cimma
burinta??
Babu abin dake warkar ko magance larura sai
halal.
Wannan haka ya ke ga sha'awa ma da Allah ya
sanya
a jikin
kowanne dan'adam mace ko namiji. An taba bani
labarin wata yarinya kan cewa wallahi duk ranar
da aka
samu akasi
bata yi zina sau 3 zuwa sama ba, to itafa ranar
babu
zaman
lafiya.
Wani idan bai sha taba ba, babu zaman
lafiya,
wani kuma shi dole sai ya zubar da jini
hankalinsa zai
kwanta. Na
ce dukka wannan karyane babu kwanciyar hankali
a cikinsu
ko daya. Dalili kuwa ''ALAA BI ZIKIRILLAHI
TADMA
INNUL QULUB''. Wallahi zikrin Allah da Karatun
Qur'ani ne
kadai zai
sanya mana peace of mind.
Idan kana son kaga ''IN TATRUKHU YALHAT WA
ILLAM
TATRUKHU YALHAT'' To dubi Mazinaci ko
mazinaciya. Hakanan idan kana neman
''UULAAI'KA KAL AN'AM,
BAL HUM
ADHAL'' Dubi mazinaci ko mazinaciya. Wani daga
cikin
magabata na kwarai, na manta ko waye amma
ina
kyautata zaton IBNUL QAYYUM ne ke cewa ''da
zaka tarawa
mazinaci
dukkanin matan duniya yayi zina da su. Sai aka
samu
matsala wata guda bata cikinsu ta zo giftawa
wallahi
sai ya
kwallafa rai akanta'' ashe karyane babu kwanciyar
hankali da
natsuwa ga zina.
Abin da ke bani mamaki da mazinaci shi ne. Kai
dan'adam ne
amma sai ka butulcewa Ni'imar da Allah yayi
maka ta
tinani da hangen nesa. Duk wacce ka yi zina da
ita, ba fa
daga sama
ta fado ba, kuma ba a kasa aka haqota ba. A'a
haihuwarta
aka yi. Dan me kai kuma zaka tozarta 'yar wasu
da
sunan wayewa. Randa aka zo ramawa akan 'yarka
wallahi
sai ka
gwammace baka zo duniya ba.
Dandai tonon asiri babu dadi ne. Dana fada
muku
mazinacin
da ya kama 'yar cikinsa da dan cikinsa suna zina.
Shi da
kansa ya kamasu ba wani ba. Wannan wa gari ya
waya?? Idan
Allah ya ce abu kaza Halal ne to kayi daidai
iyawarka
haramun kuma ka guje shi gabadaya ''MA
AMARTUKUM BIHI FA'ATU MINHU
MASTADA'ATUM WAMA NAHAKUMA
ANHU
FANTAHU'' wannan shi ne kadai zaman lafiyata
da
taka.
Mata Ubangiji ku ya fara zarga da laifin zina.
Saboda
bayyana tsiraici da kuke yi. Ki daina sanya tirare
mai kamshi
sosai
idan zaki fito, wallahi wannan ma zina ne. Dan
kuwa
tabbas
kusantar zina kike. Ki daina maqe murya a
lokacin
magana dan shima sunansa zina, ki daina caba
kwalliya ko ki
fito
babu Hijab (hijab na sharia) dan kusantar zina ne.
Ki
daina ballagazanci da rashin kamun kai. Ko
yawaita
abokai maza
musamman 'yan swagger and so on, ''WALA
TAQRABUZ
ZINA.......'' Hijab da kamun kanki ne zai sa Allah
ya
kare daga sharrin zina da fyade.
ZINA BA ZATA TABA MAGANCE MA SHA'AWA BA
SAI
DAI AURE
A ZINA BABU KWANCIYAR HANKALI
Tags:
fadakarwa

0 comments: