Thursday, 4 December 2014

ALJANU SUNA ZUWA MASA HIRA DASHI

ALJANU SUNA ZUWA MASA HIRA DASHI

Malam dan Allah mike kawo haka? Malam nine wani lokaci in ina karatun ALQUR-ANI sai inji kamar bacci ya daukeni sai in ga ina hira da wasu mutane kuma wlh in zan farka sai na farka ina murmushi da farin ciki Haka kan faru dani wani lokaci a kalla so 3 a wuni. Musamman ma da dare in ina bacci.

Akwai watarana har na tashi a zaune a kan kado ina hira da wadannan mutane sai da matata ta bubbugeni tace min dawa nike hira Sai nace da ita nike hira mana sai na koma na kwanta.

Akwai wata rana matata ta tambaye ni cewa mi yafaru jiya da dare ina ta furta kalmar sha-hada.

Toh ni dai ban bata amsa ba domin ban san amsar da zan bata ba Sai nakawo wasu magangannu wanda zata manta da wannan tambayar.

Malam dan Allah ko mice kawo haka.

(daga wani Bawan Allah ).


Abisa dukkan alamu kana tare da shafar Aljanu ne. Hasali ma su suke sanya maka wannan Barcin aduk lokacin da ka nufi yin karantun Alqur'ani. saboda bassu son kayi duk abinda zai rabaka dasu.

Su din ne suke zuwa maka acikin barci ko afarke, har suke yin hira dakai. Har ma suke firgitar dakai. har kana maganganu acikin barcinka ba tare da saninka ba.

Babbar shawarar da zan baka anan ita ce:

Ka yawaita yin karatun Alqur'ani da zikirin Allah safe da yamma.

* Ka kula da sallolinka na farillah da nafilfili da kuma addu'o'in bayan Sallah.

* Kwanciya da alwala tare da karanta Ayatul Kursiyyi, Amanar Rasoulu, Qulhuwallahu, Falaki da Nasi.

* Kula da addu'o'in cin abinci, da addu'ar fita daga gida, addu'ar kwanciyar barci, data tashi daga barci.

* Daga karshe idan abin bai dena gaba daya ba, ka daure ka ziyarci nan ZAUREN FIQHU ko kuma wata Cibiyar Kula da Lafiya ta Musulunci mafi kusa, domin adubaka, ayi maka Rukyah abaka magunguna.

Allah ya sawwake, Allah ya baka lafiya.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: