""TAKAITACCEN TARIHIN SHEIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM""
An haifi marigayi Sheikh JA'AFAR MAHMOUD ADAM a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Sunan mahaifinsa shi ne Malam Mudi dan malam Adamu, Sunan mahaifiyarsa malama Atti.
Marigayi Sheikh JA'AFAR ya fara karatunsa na Allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansa ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani malam Umaru a wani gari shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shima akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma daga shine musabbabin zuwansa KANO bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, Amma yake zaune a Unguwar Fagge a kano. Tun kafin zuwansu kano, tuni marigayi Sheikh JA'AFAR ya riga ya fara Haddar ALQUR'ANI mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.
Bayan da malam JA'AFAR ya kammala haddar ALQUR'ANI mai girma, kasancewarsa mai sha'awar Ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen MISRA a cibiyar yada Al'adun kasar MISRA, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Ebening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na Primary, amma duk da haka a wannan karatu guda biyu 2 : waccan makarantar ya je ta da Daddare bayan sallar Isha'i waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kammala wadannan makarantu a Shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar G.A.T.C. Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam JA'AFAR ya sami gurbin karatu a Jami'ar MUSULUNCI TA MADINAH, a inda ya karanta Ilimin TAFSEER da ULUMUL QUR'AN, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh JA'AFAR ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu 2 (MASTERS) a Jami'ar kasa - da - kasa Ta Africa da take Khartoum, Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri da digirgir (PHD), A Jami'ar Usman dan Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na Ilimr Akwai Malaminsa na farko, Mutumin Kasar Masar, Sheik ABDUL-AZIZ ALI AL-MUSTAFA, da kuma Malam NUHU A UNGUWAR DANDAGO, Wanda malam ya karanci Ilimin Fiqhun Malikiya da wadansu litattafai na Hadisi a gurinsa, da kuma Malam MUHAMMAD SHEHU, mutumin Lokoja, wanda malam ya karanci NAHAWU da SARFU da BALĂGA da ADAB a wajensa. Akwai kuma Sheikh ABUBAKAR JIBRIN Limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. AHMAD MUHAMMAD IBRAHIM shi ma na Jami'ar Bayero ta KANO. Daga cikin Malamansa na Jami'a kuma, akwai Sheikh ABDURAFI'U DA Dr. KHALEED ASSABT.
Daga cikin makaratun da malam ya karantar da su, sun hada da Tafsirin ALQUR'ANI mai girma, Kitabuttauhid, Umdatul Ahkam, Arba'una Hadithan, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyadussalihiin, Siratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus salaatun Nabiy.
Wasu daga cikin Daliban Malam sun hada da Malam RABI'U UMAR R/LEMO da malam SANI ABDULLAHI ABDULHAMIDI DORAYI da malam ABDULLAH USAMAN GADAN KAYA da malam SANI HARUNA da Malam IBRAHEEM ABDULLAHI SANI da malam ALI YUNUS MUHAMMAD da Dr. SALISU SHEHU da malam HAMISU KURA da malam ANAS MUHAMMAD MADABO.
Kafin rasuwarsa, Malam ya Fara gagarumin Aikin Rubuce TAFSIRINSA A harshen hausa a karkashin wannan cibiya (SHEIKH JA'AFAR ISLAMIC DOCUMENTATION CENTRE). Marigayi Sheikh JA'AFAR MAHMOUD ADAM Ya rasu ranar JUMA'A 26/rabi'ul Auwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadanst 'yan ta'adda suka kai masa, a Dai dai lokacin da yake Jagorancin SALLAR ASUBA a masallacin Juma'a na dorayi. Ya Rasu ya bar mata biyu 2 da 'ya'ya shida, yayix da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan Aiwatar da wannan Kisan gilla a kansa. DUBUN-DUBATAR MUTANE Ne daga ko'ina cikin kasar nan suka harci Jana'izarsa, kuma an binne shi ne a Makabartar Dorayi.
"ALLAH YA JI KAN MALAM JA'AFAR YA GAFARTA MASA, YA SAKA MASA DA GIDAN ALJANNAH. AMEEN THUMMA AMEEN

0 comments: