YADDA ZAKA HADA THEMES DA KANKA TA HANYAR
AMFANI DA BLUEFTP.
Abubuwan da ake bukata yayin
gudanar da wannan aikin:
1. BlueFTP: wannan shine jigon
wannan aiki domin da wannan application ne zakayi
amfani domin hada wannan themes daga farko har
karshe.
2. Pictures: sune hotonan da kake son ka hadan wannan themes dasu.
3. Themes: Dole ka tanadi wani
themes na daban domin gudanar da wannan aikin.
4.
Empty Folder: Zaka kirkiri folder sabuwa wanda babu
komai a cikinta, domin a cikinta ne duk wani tarkace zai
zauna yayin wannan aikin.
5. Nutsuwa: Ka tsaya ka nutsu
yana da matukar amfani wajen hada themes domin da kayi kuskure zai baka file corrupted.
To Bari Mu Fara:
Mataki Na 1:
ka kirkiri sabuwar folder ka sanya mata
suna.
Mataki Na 2:
sai kayi copy din hoton
an da kakeso ka hada themes din dasu zuwa cikin
wannan sabuwar folder daka sanyawa suna
Mataki Na 3:
sai ka bude blueFTP dinka. Idan farkon budewarka ne zai nuno maka tutoci, to sai ka zabi tutar
England, saika shiga.
Mataki Na 4:
Idan ka bude shi zai nuna maka phone
ko memory, kaje foldar da themes din naka yake. sai ka
zabi inda theme dinka yake, sai kaje kan themes din ka
danna OK akansa.
Mataki Na 5:
zaka ga wadansu kari-
kitai na cikin themes din kamar screensaver.png, wallpaper.jpg da dai sauransu. Saika danna menu zaka
ga wani wuri SELECT ALL ITEM saika shiga wurin, zaka ga
wani bluen abu ya rufe wadannan kari-kitan duka.
MATAKI
NA 6:
Sannan saika dana option again sai ka shiga wurin da aka rubuta EXRACT SELECTED ITEM Daga nan saika ta danna back har ka koma akan
foldar ka mai suna WIZARD , saika danna menu kaje
wurin da zaka ga EXRACT ITEM HERE saika shiga wurin. Zasu rika tambayarka kawai ka rika danna YES har ta
gama.
Mataki Na 7:
Bayan kayi extracting dinsu, zaka ga
wa dannan kari-kiran sun dawo nan, sai ka hau kan
WALLPAPER.png ta theme din sai ka danna menu ka
shiga wurin da aka rubuta RENAME, daga nan sai kayi
copy din sunan daka gani a wurin kuma saika goge WALLPAPER din. Kuma ka lura duk sunan daka gani shi
za kayi copy idan babban baki ya fara ko karamin baki, kai dai
kawai ka lura.
Mataki Na 8:
Daga nan sai kaje kan sunan
daka sanyawa hoton naka wanda kake so ya zama
sabon wallpaper ta themes din naka. Sai ka danna
menu ka shiga wurin RENAME,ka goge sunan da ka gani a gurin sannan sai ka sanya wannan sunan da nace
kayi copy dinshi a baya watokan sunan wallpaper din
themes din daka goge.
Mataki Na 9:
Haka za kai ta
maimaita wannan matakin na 8 akan duk hoton da
kake so ka canza mashi hoto a matsayin sabon wani abu a cikin themes din.
Mataki Na 10:
Bayan ka gama saika danna menu sannan ka shiga SELECT ALL.
Mataki
Na 11:
Daga nan saika danna menu sai ka shiga wajen
COMPRESS.nth idan nokia gareka ko kuma ka shiga
wajen COMPRESS.thm idan sony ericsson gareka. Daga
nan zai nuna maka File.nth sai ka goge iya file, sai ka
sanya sunan da kake.misali Nasir.nth saika da Ok. Zai nuno maka Compress Done.
Mataki Na 12: shikenan ka
gama sai ka fito/rufe BlueFTP dinka, Kaje Wajen da
Wannan Folder taka mai suna WIZARD take ka shiga
zaka ga THEMES din da ka hada da sunan da ka sanya mashi.
Duk tambayar da aka yi
maka zaka amsa da YES ne, kuma karda kayi garajen
Danna YES. Domin Idan Kayi Gaggawa Duk Nisan Da Kayi Zai Lalace Gaba Daya...
Don Haka Sai A Kiyaye.
GARGADI:
Dole ne ka goge asalin hoton themes din bayan da kayi
copy din sunan a mataki na 7, domin kaucewa double
copy da invalid themes da kuma corrupted theme.
Note:
Wannan themes na masu nokia java.eg
C1,C3,2700,X2.Asha,Express Music,3110 da dai sauran java phone. da masu sony ericsson zasu iya hada
shi...masu symbian banda ku a ciki.
YADDA ZAKA HADA THEMES DA KANKA TA HANYAR AMFANI DA BLUEFTP.
Tags:
waya and computer

0 comments: