YARO TSAYA MATSAYINKA KADA ZANCEN YAN
DUNIYA YA RUDE KA
An yi wadansu samari su uku a wani gari wai shi
Kona, guda ana kiransa Halilu Wayo, guda Abdu
Lura, karamin kuwa Nahi’u Hankali. Ba banza ba
aka lakaba musu wadannan sunannakin, sai don
ko wanne halinsa ya dace da a kira shi hakanan.
Suna nan sai ran nan Halilu Wayo ya ce, “Ya
kamata mu shiga duniya, mu gwada wadannan
baiwa da Allah ya yi mana. Mu ga wanda ya fi,
don saura su sakam masa. Amma yanzu ina
amfanin muna zaune kurum, kullum sai gardama
ta fatar baki?” Saura suka ce, “Halilu, aiko
gaskiyarka. Da ma an ce maza- dangin gujiya ne,
sai an fasa a kan san bidi.” Suka shirya, suka
dunguma zuwa Bila.
Da suka isa suka nemi su ga Sarki, aka yi musu
iso. Suka tafi, suka fadi suka yi gaisuwa.
Dogarawa suka amsa, Sarkin Zagi ya tambaye su
sunayensu da sana’arsu, da inda suka fito da
kuma inda za su. Suka fadi sunayensu dai dai,
suka gaya masa kuma sun fito daga Kona ne, za
su yawon duniya, don ko Allah ya sa su sami inda
za su raba gardamar da ke tsakaninsu.
Sarki ya yi dariya da ya ii sunayensu, sa’an nan
ya dube su, ya ce, “Wace gardama ta rabo ku da
gida?”
Halilu ya ce, “Ni da Allah ya ba wayo, tsammani na
ke duk ba abin da ya fi wayo amfani cikin zaman
duniya. Wannan kuwa Abdu tsammani ya ke ba
abin da ya fi lura amfani ga mutum. Dan saurayin
nan kuwa Nahi’u shi cewa ya ke ba a gama
hankali da kome. Saboda haka muka fito dai, mu
sami inda za mu raba wannan gardama mu huta.”
Sarki ya ce, “I, ai ko lalle wannan gardama ta isa a
rabo da gida, a shiga duniya neman inda za a raba
ta.”
To, Sarkin nan kuwa na kiwon balbelu kamar dari.
Ka san yadda balbelu su ke, duk kamarsu daya ce,
amma duk da haka a cikin balbelun nan akwai
wata wadda Sarki ya ke so. Ba don kome ba kuwa,
sai don ita ta fi amincewa da mutane. Kullum da
ta ga azahar ta yi an taru wurin fadanci, sai ta
rabo da ‘yan’uwa ta zo kusa da Sarki, ta tsaya
yana wasa da ita. Ko da ya ke an saba da ganinta,
duk da haka da tashi ta shiga cikin ‘yan’uwa ba
mai sake fid da ita, don yawansu da kuma
kamanninsu da ya ke daya.
Yan samarin nan sun gama gaya wa Sarki
labarinsu ke nan, sai ga balbelan nan ta taso fir, ta
sauka bisa kan karagar Sarki. Da Sarki ya dube ta
sai ya ce, “Alhamdu lillahi, ga ma inda za ku raba
gardamarku, ku huta da wahalar shiga duniya. ‘‘
Ya kamo balbela ya mika musu, ya ce, “To, kowa
ya yi amfani da baiwar da Allah ya yi masa, ya
san yadda zai yi ya gane balbelan nan, ko ta shiga
cikin dubun balbelu.”
Abdu ya lura da irin siffarta da kyau, tun daga
kafafunta har ya zuwa bisa kai. Nahi’u Hankali
kuwa bai ko dube ta ba. Ashe kuma sa’ad da Abdu
ke lura da irinta, Halilu Wayo ya kaikaici idanunsu
ya zuba mata ruwan goro a fiffike. Da suka jima da
ita a hannu, Sarki ya ce su sake ta. Suka sake ta,
ta tashi.
Sarki ya ce, “Na sa fam biyar, da dawaki biyar, da
rakuma biyar, da shanu biyar, da bayi biyar, duk
wanda ya gane ta zan ba shi. Bayan haka kuma in
gina masa gida, in nada shi Sarkin Fadana.”
Samarin suka ce, “To, mun ji, mun ko gode, Allah
ya kai mu gobe.”
Gari na wayewa, balbelu suka taru makil a kofar
gidan Sarki inda a ke ba su abinci. Wani bawa mai
lura da su ya fita ya ba su abinci. Sarki ya kira
samarin, ya ce, “To,
ga su can waje, wa zai fara
zuwa?” Halilu Wayo ya ce shi zai fara. Daren nan
kuwa an kwana ana ruwa, saboda haka dan yawun
goron da ya zuba ya wanke. Ya nema, bai gane ta
ba, ya dawo, ya ce ya kasa, wani ya tafi.
Sarki ya dubi saura, ya ce, “Wa zai bi?” Sai Abdu
Lura ya ce za shi. Ya tashi ya tafi, sai ya iske
ashe abubuwan da ya lura da su a jikinta, duk
galibinsu ko wacce na da wadannan abubuwa.
Da ya ga ya rude, ya kasa gane ta, sai ya ce, “Kai,
wace ce ke son Sarki cikinku?” Su duka suka
amsa, “Ni, ni!” To, ganinka wa zai ce ba ya son
ubangijinsa, mai lura da shi kwarai?
Da ya ga dai bai samu abin kamawa ba, sai ya
koma, ya ce ya kasa. Sarki ya yi murmushi, ya
dubi Nahi’u Hankali, ya ce, “In ta bi daga daga na
kurya ka sha kashi.” Sai Nahi’u ya tashi ya tafi.
Da isarsa sai ya dube su, ya rike baki wai shi
al’ajibi, ya ce, “Kai, ai ko jiya kun kwana kuna
waka, amma wannan da ta je wurin Sarki jiya da
azahar, ya nuna su da baki, ya ce, “ta fi kowa
murya.”
Ko da balbelan nan ta ii an yabe ta, sai ta ce,
“Haba samari, don ma ka tarad da ni na tsufa. Da
sa’ad da na ke yarinya ce, in na fara waka ai kowa
sai kallo.”
Nahi’u ya ce, “Ai lalle da alama.” Ya sa hannu ya
kama ta, ya dauka ya kai wa Sarki. Da Sarki ya
gan ta, ya yi mamakin yadda saurayin nan ya gane
ta. Ya kawo duk abin da ya ce, ya ba shi, ya kuma
nada shi Sarkin Fada. Saura kuma suka shiga cikin
fadawan Sarki. Sarkin Fada Nahi’u ya yi musu
kyauta daga cikin abin da ya samu. Suka yi
aurarraki, suka zauna nan, su da garinsu sai sako
ko yaushe wurin iyayensu.
Ran nan da dare suna zaune da Sarki, sai wani
maroki ya zo yana ta bunkasa Sarki da kirari,
har
Sarki ya shiga cikin abinda ya ke fadi, sai Sarkin
Fada ya ce, “
Allah ya ba ka nasara, ka ga fa da
irin wannan bunkasarwa ne har na yaudari
balbelarka ta tona kanta.”
Sai Sarki ya yi sanyi da
bin zancen maroka da na makada.
YARO TSAYA MATSAYINKA
Tags:
Abin Mamaki

0 comments: