Tuesday, 7 April 2015

ALAMOMIN SON MANZON ALLAH (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM) A MAHANGA TA ILIMI

ALAMOMIN SON MANZON ALLAH (SALLALLAHU
ALAIHI WASALLAM) A MAHANGA TA ILIMI

Malamai
sukace Abubuwa hudu 4 suna daga Alamar son
ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam)
1- ﻃﺎﻋﺘﻪ ﻓﻴﻤﺎﺍﻣﺮ
*Yi maSA biyayya cikin dukkan umarninSA.
2- ﺗﺼﺪﻳﻘﻪ ﻓﻴﻤﺎﺍﺧﺒﺮ
*GaskataSHI cikin abinda ya bada labari.
3- ﺇﺟﺘﻨﺎﺏ ﻣﺎﻧﻬﻰ ﻋﻨﻪ ﻭﺯﺟﺮ
Nesantar duk abinda yayi hani akansa kuma ya
tsawatar.
4- ﺃﻻﺗﻌﺒﺪﻭﺍﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻﺑﻤﺎﺷﺮﻉ
Kada kubautawa Allah face da abinda ya
Shar'anta.
Wannan shine sharadai wadanda cikasu shine
yake nuna Alamar son ANNABI (Sallallahu Alaihi
Wasallam), komai kakeyi idan kaji ance ANNABI
(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace; ya zama wajibi
ka tsaya kaduba kaga naka ya dace danaSA?
Idan ya dace sai ka cigaba idan ya sa6a sai
kabar naka kadau naSA.
Zancen kowa ka aunashi da zancensa idan ya
dace kadauka idan ya sa6a kabarshi.
Wani mai hikima acikin baitikansa na yabon
ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam) da harshen
Hausa yake cewa:
*IN MA'AIKI YAYI ZANCE,
BA BUKATAR WANE YACE,
SAI KA YARDA KA KO AMINCE,
BA TARE DA NUNA GARDAMA BA.
Yana daga cikar son ANNABI (Sallallahu Alaihi
Wasallam) karmu kuskura mu yanke wani hukunci
cikin wani zance ko wani aiki sai ya dace da
naSA (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Don Haka Maulanmu Shehu Ibrahim Niasse (Rta)
yace:
ﺇﺫﺍﺻﺎﺭﺧﻴﺮﺍﻟﻨﺎﺱ ﺻﺮﺕ ﻭﺭﺍﺀ ..."
ﻭﺇﻥ ﺣﻞ ﻳﻮﻣﺎﻓﺎﻟﻤﺼﻴﺮﺑﻌﻴﺪ ,
Shehu (Rta) yace Idan mafi alkairin Halitta ya tafi
cikin wani aiki ko zance ni kuma sai na zamo
bayanSA cikin aiki da magana wajen Isar da
sakonSA.
Idan kuma ya tsaya ga barin yin wani aiki ko yin
magana cikin wani hukunci to nima
matafiya tayimun nisa cikin aikatawa, wannan
shine alamar son ANNABI (Sallallahu Alaihi
Wasallam)
sannan Yana daga alamar sonSA yawaita
anbatonSA ko yawaita yimaSA salati lokacin da
kaji waninka ya ambaceSHI. Malamai sukace:
ﻣﻦ ﺃﺣﺐ ﺷﻴﺌﺎ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻦ ﺫﻛﺮ ﻩ
*Duk Wanda yaso wani Abu to ya yawaita
anbatonsa, da wannan ne Shehu Ibrahim Niasse
(Rta) ya gagara yake cewa cikin wani baitinsa:
ﻓﻮﻗﺘﻲ ﻭﺳﺎﻋﺎﺗﻲ ﺻﺮﻓﺖ ﻟﺬﻛﺮﻩ @
ﺻﻼﺓﻭﻣﺪﺣﺎﻣﻨﻪ ﻗﺪﺻﺮﺕ ﺟﻴﻠﻤﺎ @
Shehu (Rta) yace; "Dukkanin lokutansa ya
maidasu cikin Ambaton ANNABI (Sallallahu Alaihi
Wasallam) da yimasa salati da yabonSA. Shiyasa
na zamo mai cikar girma wajen Allah.
Wannan shine takaitaccen abunda ya sawwaka
inda na kuskure dama ni mai rauni ne wajan da
Aka dace kuma shine daga Allah (S.W.T).
VIA: SYD ABUL-INYASS ABDULHADI (RTA)
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: