Wednesday, 8 April 2015

LABARIN WATA YARINYA DA LADANI A MASALLACI

LABARIN WATA YARINYA DA LADANI A
MASALLACI

wata yarinya kyakkyawa yar masu hali,
wata rana bayan sallar isha'i tayi shirin zata
kaiwa antinta ziyara a wata unguwa nan kusa
dasu....
Ta fito daga gidansu tayi nisa kenan sai wata irin
guguwa ta taso mai karfin gaske, ta rasa inda
zatasa kanta sai taga wani masallaci a bude sai
ta ruga ta boye aciki ta zauna bangaren mata......
Tana nan ciki har dare yayi sosai guguwa dai
bata lafa ba... Can sai ladanin masallacin yazo
kafin ya rufe masallacin sai yaga kyakkyawar
yarinya a ciki...
To dama shidai ladanin ya kasance mutum ne
matashi mai ilimi da tsoron Allah....
Koda ganinta sai yace tayi sauri ta fita dan kar
wani mummunan abu ya shiga tsakaninsu... Sai
yarinyar ta rokeshi cewa dan Allah ya barta ta
zauna aciki dan bata san inda zatasa kanta ba...
Sai ya barta, shi kuma ya koma can gefe daya
daga cikin masallacin ya bude littafi yana
karatu... Ita dai yarinya ta kasa runtsawa balle
tayi barci...
Wani abin mamaki data gani shine idan mutumin
yayi karatu sai taga ya dora hannunsa a wutar
kyandir bazai cire hannunsa ba har sai wutar ta
kusa mutuwa, haka yake tayi tsawon daren nan
har fitowar alfijir.....
Can sai ya tashi ya kira sallah, sannan yace mata
to sai ki fita ki tafi kafin jama'a su fito....sai tace
to amma zanso nasan wani abu, dan Allah me
yasa lokacin dakake karatu cikin dare sai inga ka
dora hannunka akan harshen wutar kyandir?
Sai ya amsa mata yace dalilin da yasa nake dora
hannuna akan wuta shine, kinga muna tare mu
biyu kadai, kuma shedan yana samin kokwanto
sha'awata tana kara karfi duk lokacin dana dora
hannuna akan wutar kyandir sai in tuna a raina
cewa wannan fa bakomai bace idan aka
dangantata da wutar JAHANNAMA, to sai in sami
natsuwa...
yarinya ta tafi gida tana mamaki, sai ta
labartawa iyayenta duk abinda ya faru da ita,
sannan kuma tace musu ta sami mijin
aure....tace mutum mai tsoron Allah shi kadai ne
zai iya kare hakkin matarsa... Atakaice dai
talakan ladanin nan shi ya aureta.
TO JAMA'A KU DUBA KUGANI,
BAWAI DAN KYANSHI KO ASALINSHI YASA YA
SAMETA BA SAI DON TSORON ALLAH... HAKIKA
DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, ALLAH ZAI
AZURTA SHI TA INDA BAYA ZATO.
YA ALLAH KA AZURTAMU DA TSORONKA ACIKN
ZUKATANMU.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: