Wednesday, 8 April 2015

wani labari karanta A Nutse kasha labari

labarin ya fara ne lokacinda wani sarki da akayi a
bani'isra'ila yayi ta damfara da yaudarar talakawar sa cewa
shi Allah ne.
kuma yana yin hakanne ta hannun wani boka na shi da yake
koya masa tsafinda yike yi domin mutane su yadda Shi Allah
ne,
Wata rana bokannan ya kira wannan sarkin ya fada masa
cewa:lallai girma ta kamani, ina so Ka samu wani yaro mai
kokari wanda zan rika koya masa wannan sihirin saboda
gudun bayanni na mutu zai cigaba daga Inda na tsaya.
sunyi sa'a na samo wani yaro mai kokari Inda ya fara zuwa
daukan darasi, saidai akan hanyarsa yakan ji sautin wani
mutum mai bauta acikin wani kogo, wanda yana fadin
wadansu kalmomi,
Wata rana yaro yace kai bari dai in leka wannan kogon
domin in gani wani mutum ne wannan?
bayan shigar yaro keda wuya, sai ya samu wannan mutumi
a gurfane yana bauta.
wannan mutumi ya tambaye yaro, kai yaro daga ina mai ya
kawo Ka Nan?
yaro ya kwashe duka labari ya fada masa. Nan take malami
ya samu shawo kan wannan yaro akan wannan abu da yake
kai ba gaskiya bane, komawa ga Allah shine gaskiya, yaro
abu dai bai gama shiga kunnuwar sa ba, malami yace : da
yaro duk sanda zaka wuce kazo mu rika Karatu hakama idan
zaka koma.
haka su kayi tayi,
sai kowannen su (sarki da mai koya sahiri) suka fahimci
wannan yaro al'adunsa suna canzawa, kuma yakan dade.
sunyi kokarin daukan mataki har da duka akansa, amma
hakan baisa ya canja halin NASA ba.
domin malamin ya koya masa dibara
na cewa: duk wanda yace masa ya dade yace rike shi aka yi
wurin koyan tsafi.
masu Karatu kuyi hakuri domin zamu gintse labarin saboda
tsawon sa amma zamu cigaba cikin izinin Allah.
kuma zamuyi tambayoyi bayan gama labarin.
Allah yasa mu dace.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: