GA WANI MUMMUNAN FASIKANCI
Assalamu alaikum 'Yan uwa.
Akwai wata MUMMUNAR BARNA
TA FASIKANCI
wacce ta bullo kwanan nan cikin
al'ummah.
Zaka ga samari da 'yanmata
(Musamman
wadanda aka sa ranar aurensu)
suna zuwa suna
daukar wasu munanan HOTUNA
MARASA KYAN
GANI.
Ko kaga sun rungumi juna, ko
kaga Saurayin ya
dora fuskarsa akan Qirjin
budurwar, ko kaga
budurwar ta zauna akan cinyar
saurayin, ko kuma
ka ganta ta dora tafin
hannayenta akan kafadar
Saurayin ko Kan Qirjinsa.
Wannan ba Qaramar Fitsara da
Fasikanci bane,
Kuma WALLAHI BIL-LAHIL AZEEM
Duk ma'auratan
da suka aikata irin wannan kafin
aurensu, to SUN
ZUBAR DA ALBARKAR AURENSU.
Kuma sunci
amanar Allah da Manzonsa, sun
wulakantar da
tarbiyyar addininmu na Islama.
Haramtaccen Jima'i ba shine
kadai ZINA ba.
kallon da ya sa'ba ma shari'a ma
ZINA ne. Ta'ba
jikin juna kafin aure ma ZINA ne.
Yin kalamai na
BATSA ko zantukan motsa
sha'awa shima ZINA
ne.
Duk Ma'auratan da suka aikata
'daya daga cikin
wadannan, to tabbas SUN ZUBAR
DA ALBARKAR
ZURIYAR DA ZASU HAIFA.
Nagartar iyaye da kuma
albarkarsu tana shafar duk
irin zuriyar da zasu haifa.
Hakanan lalacewar iyaye
da kuma fasikancinsu yakan
shafi irin zuriyar da
zasu haifa.
Kunyi zina kafin aurenku, kuma
yanzu kuna
tsammanin zaku haifi
Hamshakan Malamai da
Mahaddatan Alqur'ani?
Yayi fasikanci dake tun kina
gidanku, ya riga ya
sanki 'ya mace tyn kafin aure,
kuma kina zaton zai
rike ki da mutunci bisa amana,
bayan ya riga yaci
amanar Allah da Manzonsa?? Ta
ki amanar ne ba
zai ci ba??
Duk abinda kuka shuka shi zaku
girba.. komai
kankantarsa komai girmansa.

0 comments: